Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » ALLAH YA YI WA SHAHARARREN DAN DAMBEN GARGAJIYA ALH YAHAYA BARGAJA ,BAGOBIRI RASUWA
    Traditional/tourism

    ALLAH YA YI WA SHAHARARREN DAN DAMBEN GARGAJIYA ALH YAHAYA BARGAJA ,BAGOBIRI RASUWA

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanJune 22, 20262 Mins Read
    IMG 20260622 WA0068
    IMG 20260622 WA0068

     

    Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un!

    Allah SWT ya yiwa shahararren ɗan damben gargagajiyar nan, Alh. Yahaya Ibrahim Bargaja da aka fi sani da Bagobiri Ɗantcimau rasuwa.

    Sanarwar rasuwarsa na kunshe cikin wata sanarwar da Alh Ibrahim Mohammad danmadamin Birnin Magaji ya rabawa manema labarai.

    Sanarwar ta ce y a rasu ranar Litinin, 22/06 /2026 sanadiyar rashin lafiyar da yayi fama da ita a garinsu wato Bargaja dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Isa ta Jihar Sakkwato.

    Ɗan shekara 86 a duniya, Alh. Bagobiri Ɗantcimau ya yi shuhura a fagen damben gargagajiya musamman a ƙarshe ƙarshen shekarun 1960s zuwa 1970s da 1980s yadda har shahararren Makaɗin Damben ƙasar Hausa Marigayi Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan’anace Yartsakkuwa, Gandi Sakkwato ya yi masa waƙa mai amshi “Yaƙi sabon Bagobiri, mai kayan hwaɗa”.

    A lokacin rayuwarsa ta dambe ya fafata da yan dambe irinsu Umaru Gundumi na Karime da Arnen Ɓalli da Audu Kure da Lawai Basafce da Maigari ba Imani da Ɗankincimi da Ado Ɗankore da Mushe da Gadede da Goto da Kundi da Shagon Wanke da sauran su.

    Anyi jana’izarsa a garin nasu wato Bargaja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ya bar iyali da yan uwa da dama.

    A cikin watan Afrilu na wannan shekara (2026) ya halarci bikin buɗe taron ƙasa akan tarihin rayuwa da waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace Yartsakkuwa, Gandi Sokoto da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto ta shirya a birnin Sokoto tare da abokin fafatawarsa, wato Umaru Gundumi.

    Allah SWT ya jiƙan sa da rahama shi da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

     

     

     

    bagobiri dambe Dan rasuwa SHAHARARREN
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleA Moment of Hope for Gombe State*
    Next Article Yobe Govt, UNICEF procure $200,000 RUTF to tackle malnutrition

    Related Posts

    Traditional/tourism

    VP Shettima, Governor Zulum, royal fathers storm Lafia for emir’s 70th birthday, commission projects

    June 22, 2026
    Traditional/tourism

    Etsu Nupe Confers Madakin Raya Kasar Nupe Title on Sen. Sani Musa

    June 21, 2026
    Traditional/tourism

    Governor Radda’s Aide, Matazu, Receives “Sarkin Hausawan Sudan” Traditional Title

    June 9, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026244 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026231 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026183 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026149 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026149 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026136 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.