Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»Amfani da motocin da ke amfani da man gas na CNG Ya Fara Sauya Kudin Sufuri a Najeriya — Tinubu
    News

    Amfani da motocin da ke amfani da man gas na CNG Ya Fara Sauya Kudin Sufuri a Najeriya — Tinubu

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 21, 20262 Mins Read
    FB IMG 1790024188265
    FB IMG 1790024188265

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce amfani da CNG wajen sufuri ya fara rage wa ’yan Najeriya kuɗin mota a wasu jihohi, inda ya bayyana cewa ƙarin jama’a za su fara ganin sauƙin kuɗin sufuri daga 1 ga Oktoba, 2026. Ya ce a Borno, motocin CNG da na lantarki na jigilar jama’a kan N50 zuwa N100, maimakon N300 zuwa N600 da ake biya a wasu motocin kasuwanci, yayin da a Kaduna motocin CNG guda 100 suka kwashe kusan fasinjoji miliyan 3.2 a shekarar farko, tare da ceton sama da N3.5 biliyan ga matafiya.

    Tinubu ya ce a Oyo, motocin CNG na Pacesetter Transport sun sauke kuɗin mota daga Lagos zuwa Ibadan daga kusan N8,000 zuwa N3,200, yayin da a Adamawa aka rage wasu kuɗaɗen sufuri da kusan kashi 50 cikin 100. A Enugu, kuɗin mota daga Enugu zuwa Nsukka ya sauka daga N2,500 zuwa N1,500, sannan a Plateau motocin da gwamnati ke tallafawa suna jigilar kusan mutane 13,000 kullum kan N200, idan aka kwatanta da sama da N500 da ake biya a motocin kasuwanci.

    Read also: PRESIDENT TINUBU MOURNS FORMER LAGOS DEPUTY GOVERNOR SEN. IDIAT ADEBULE

    Read also: COAS JOINS PRESIDENT TINUBU, CDS, SERVICE CHIEFS IN PAYING LAST RESPECTS TO FALLEN NAF 931 CREW

    Shugaban ya ce irin wannan sauƙin ya kuma bayyana a Abuja, inda haɗin gwiwar gwamnati da NURTW ya samar da rangwamen kashi 40 cikin 100 ga fasinjojin wasu hanyoyin da motocin da aka sauya zuwa CNG ke bi. Ya ce kuɗin mota daga Area 1 zuwa Gwagwalada ya ragu daga N1,500 zuwa N900, Nyanya daga N700 zuwa N420, yayin da Wuse ya sauka daga N400 zuwa N240. Ya ƙara da cewa a cikin shekaru uku, an sauya sama da motoci 120,000 zuwa CNG, tare da cibiyoyin sauya motoci sama da 400 da tashoshin CNG sama da 90 a faɗin ƙasar.

    Read also: Just In: PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU SIGNS FOUR BILLS INTO LAW AS PRESENTED TO HIM BY THE HOUSE OF REPRESENTATIVES.

    Tinubu ya buƙaci jihohi su ƙara kaimi wajen faɗaɗa shirin kafin 1 ga Oktoba, yana mai cewa Najeriya na da isasshen gas da za ta iya rage dogaro da farashin man fetur da dizal na duniya. Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa faɗaɗa ababen more rayuwar CNG da sauya motoci, domin tabbatar da cewa tanadin da ake samu daga makamashi mai rahusa ya koma ga jama’a ta hanyar rage kuɗin sufuri.

    Sabuwar Nigeria.

    buses cng fares reducing transport
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleFive ABU academic staff round off diploma programme in preparation for Masters and Fellowship in implantology
    Next Article Governor Abba Mourns the Passing of Sani Lawan Kofar Mata

    Related Posts

    News

    PRESIDENT TINUBU MOURNS FORMER LAGOS DEPUTY GOVERNOR SEN. IDIAT ADEBULE

    November 28, 2026
    News

    Just In: PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU SIGNS FOUR BILLS INTO LAW AS PRESENTED TO HIM BY THE HOUSE OF REPRESENTATIVES.

    November 28, 2026
    News

    S A To Gov. IDRIS’Extends Humanitarian Service, Donates Motorised Borehole To Community In Dakingari.

    November 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.