Daga Aliyu Samba
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar ISWAP, tare da kwato makamai da kuma ceto wani ɗan ƙasar Kamaru da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da shi a Jihar Borno.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce rundunar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton ayyukan soji da suka gudana cikin sa’o’i 24, wanda aka fitar ranar Talatan nan.
A cewar rahoton, dakarun Bataliya ta 151 sun ceto ɗan Kamarun ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar 17 ga Agusta.
An ce ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mutumin ne a ƙauyen Ashigashiya, da ke tsakanin Gwoza a Jihar Borno da iyakar Kamaru.
Rundunar ta ce an kai wanda aka ceto hannun sojoji domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace.
A Jihar Adamawa kuwa, dakarun Bataliya ta 232 da aka jibge a Garaha, Ƙaramar Hukumar Hong, sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa mambobin ISWAP ranar 16 ga Agusta.
Rahoton ya ce dakarun, tare da haɗin gwiwar mafarautan yankin, sun kuma cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa abokin hulɗar ‘yan ta’addan, yayin da yake karɓar magani sakamakon raunin harbin bindiga.
Daga hannun waɗanda ake zargin, sojojin sun kwato wayar hannu guda, katin SIM, baka da kibau guda biyu, takobin ƙirar gida guda da kuma bindigogi ƙirar gida guda huɗu.
A wani samame kuma, dakarun Bataliya ta 151 sun gano wata bindigar AK-47 da aka binne a cikin ƙasa a ƙauyen Ngurusoye, Ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
Rundunar ta ce an gano bindigar ce yayin da dakarun ke gudanar da sintirin gona, daga bisani aka miƙa ta ga hukumomin soji da abin ya shafa.
Ta ce waɗannan ayyuka na baya-bayan nan na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin sojoji na tarwatsa hanyoyin sadarwa da safarar kayayyaki na ‘yan ta’adda, tare da hana su zirga-zirga cikin walwala a yankin Arewa maso Gabas.
Rundunar ta ƙara da cewa tana haɗa hare-haren soji da sintirin da ake gudanarwa bisa bayanan sirri, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na yankin domin hana ‘yan ta’adda samun damar shiga al’ummomi.
Ta ce kwato makamai da cafke waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci zai taimaka wajen gudanar da bincike kan ayyukan ‘yan ta’adda da kuma hanyoyin sadarwar da ke taimaka musu.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’ummomi da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci dasauran miyagun laifuka.

