Ƙungiyar Matan Arewa 4 Tinubu Again (MATA) ta bayyana aniyarta ta ƙara wayar da kan mata da tattara goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce dandazon mata daga sassa daban-daban sun hallara a Kano domin ƙaddamar da ƙungiyar Matan Arewa 4 Tinubu Again (MATA), wadda ta bayyana aniyarta ta tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Read also: Gov. Abba K. Yusuf set to flag-off 2027 campaign sunday in Rogo
Bikin ƙaddamarwar, wanda ya haɗa da bikin bayar da lambobin yabo ga wasu masu ruwa da tsaki a harkokin yaɗa labarai, ya samu halartar mata masu goyon bayan gwamnatin Tinubu, da shugabannin siyasa da sauran manyan baƙi.
Ƙaddamar da ƙungiyar na zuwa ne a wani mataki na shirya mata a Arewa domin ƙara shiga harkokin siyasa, wayar da kan al’umma da kuma ƙarfafa goyon baya ga takarar Shugaba Tinubu a zaɓen da ke tafe.
A wajen taron, Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Rediyo da Watsa Labarai, Hajiya Rahma Abdulmajid, wacce ita ce Shugabar kungiyar ta MATA, ta yi kira ga al’ummar Arewa da su goyi bayan kammala wa’adin mulkin shekaru takwas da Kudu ke yi, tana mai cewa mutunta tsarin karɓa-karɓar mulki zai taimaka wajen kiyaye zaman lafiyar Najeriya da haɗin kan ƙasa.
Rahma ta bayyana cewa tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu ya taimaka wajen tabbatar da daidaito a siyasar ƙasar nan, don haka bai kamata a yi watsi da shi saboda muradin wani ɗan siyasa ba.
Read also: Governor Radda Assures APC Northwest Reconciliation Committee of Party Unity
Ta ce Arewa ta riga ta amfana da wa’adin shekaru takwas na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, daga 2015 zuwa 2023, saboda haka ya dace a mutunta damar da Kudu ke da ita a yanzu ƙarƙashin Shugaba Tinubu.
Ta ƙarfafi mata da sauran masu ruwa da tsaki da su taka rawar gani wajen wayar da kan jama’a game da muhimmancin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Darakta-Janar na Yaɗa Labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wakilta, ya jaddada cewa adalci da bai wa kowane yanki dama su ne ginshiƙan haɗin kan Najeriya.
Shi ma tsohon Gwamnan Jigawa kuma tsohon Ministan Tsaro, Malam Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan raya ƙasa da dama a Arewa, musamman a fannonin sufuri da kiwon lafiya.
Ya ambaci wasu sassan babbar hanyar Abuja-Kaduna-Kano, hanyar Kaduna-Pambeguwa, hanyoyi a Jihar Kano da gadar Jimeta a Yola, tare da wasu cibiyoyin lafiya da ayyukan inganta asibitoci a jihohin Arewa.
Ƙaddamar da MATA na ƙara fito da rawar da mata za su iya takawa wajen shiga harkokin siyasa da shirya al’umma, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tare da haɗin kan mambobinta da sauran masu goyon baya, ƙungiyar ta bayyana kanta a matsayin wani dandali na mata a Arewa da ke son ganin Shugaba Tinubu ya samu wa’adi na biyu.





