Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»Shugaba Tinubu ya jinjina wa Sarkin Saudiyya bisa samun damar shiga Ka’aba domin gudanar da addu’a
    News

    Shugaba Tinubu ya jinjina wa Sarkin Saudiyya bisa samun damar shiga Ka’aba domin gudanar da addu’a

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanNovember 2, 20266 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1793606230840

    Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada ƙudurinsa na gina Najeriya mai wadata, tare da zuba jari a makomar matasa da kuma gudanar da mulki bisa ƙa’idojin Allah da muradun al’ummar ƙasar.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake tsokaci kan ziyarar ibadar Umrah da ya kai Ƙasar Saudiyya, inda Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, mai kula da Masallatan Harami guda biyu na Makkah da Madinah, ya ba shi da tawagarsa ta Najeriya damar shiga cikin Ka’aba domin yin addu’a.

    Read also: Tinubu Honours 25 Victims Of NAF 931 Aircraft Accident, Donates Houses, N100m To Each Deceased Family*

    Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya yi addu’ar godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa ni’imar ba shi damar jagorantar Najeriya a matsayin Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ƙasar.

    Sheikh Dahlulah Muthawal na Masjidil Haram ne ya jagoranci Shugaban Ƙasar zuwa cikin Ka’aba.

    Tinubu ya miƙa godiyarsa ga Sarki Salman da Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman, bisa wannan dama ta musamman da suka ba shi da sauran ’yan tawagarsa ta Najeriya.

    Ya bayyana shiga cikin Ka’aba a matsayin wani tarihi mai muhimmanci da ba zai taɓa mantawa da shi ba, wanda kuma ke nuna kyakkyawar dangantaka, mutunta juna da haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Saudiyya.

    Shugaban ya ce: “Ina so in yi babbar godiya bisa wannan amana da girmamawa da aka nuna mana. Ban yi tsammanin zan ga shingen Ka’aba mai launukan kore da fari ba, waɗanda suka tuna min da asalin tutar Najeriya.

    “Ina godiya ga Yarima Mai Jiran Gado da duk masu gudanar da harkokin wannan ƙasa mai tsarki bisa karɓar baƙuncinmu da girmamawar da aka yi mini a matsayina na shugaban tawaga da shugaban ƙasa.

    “Dukkanmu muna fuskantar ƙalubale da adawa a kasashe kewayenmu. Za mu shawo kansu ta hanyar dogaro da Allah Maɗaukakin Sarki. Zan ci gaba da godiya har abada.”

    Ya ƙara da cewa damar shiga cikin Ka’aba wani babban karamci ne da aka yi masa, yana mai cewa: “Wannan abin girmamawa ne da na samu, kuma karamci ne daga gare su da suka ba ni damar shiga cikin Ka’aba. Wannan tarihi ne.”

    Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya roƙi Allah ya ba shi hikima da juriya domin ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima, yana mai nuna yakinin cewa Allah ya amsa addu’arsa.

    Ya ce: “Na roƙi Allah ya ba ni hikima da juriya domin ci gaba da yi wa jama’a hidima. Na san an amsa wannan addu’a. Kafin zaɓen 2023, na yi irin wannan ibada, na roƙi Allah ya karɓi Umrah ta, kuma Ya karɓa. Na yi alƙawarin cewa zan dawo domin gode Masa.”

    Da yake tsokaci kan saƙon Alƙur’ani mai girma a cikin Suratu Aali Imran, aya ta 26, wadda ta tabbatar da cewa Allah ne Mamallakin mulki, Yana ba wanda Ya so iko, kuma Yana karɓe shi daga wanda Ya so, Shugaban ya ce mulki amana ne da ya kamata a yi amfani da shi cikin gaskiya da hidimar al’umma.

    Read also: 2027: After Clerics, Barau Mobilises 3,405 Traditional Rulers in Kano for Tinubu, Abba, Other APC Candidates

    Ya jaddada cewa babu wani matsayi na iko da yake dawwama, domin Allah ne mamallakin dukkan iko da mulki.

    Tinubu ya ce: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Maɗaukakin Sarki. Shi ne Mai bayarwa kuma Mai karɓa. Shi ne Mamallakin iko da mulki. Yana cewa idan Na ba ka iko, ka yi amfani da shi yadda ya kamata. Idan ba ka yi amfani da shi bisa umarnina ba, Zan iya karɓe shi daga gare ka in ba wani. Ni kaɗai ne nake da wannan iko.”

    Shugaban ya bayyana cewa imaninsa da Allah ya ƙara masa tabbacin cewa zama shugaban Najeriya wata babbar ni’ima ce da dole ne ya mayar da ita hidima ta gaskiya ga ƙasa.

    Ya ce: “Na yi imani da hakan, kuma na yi imani ƙwarai da gaske cewa Allah Ya yi mini da ƙasata wata babbar ni’ima. Daga cikin miliyoyin mutane, a ba mutum damar zama Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Soji, wannan ni’ima ce da Allah kaɗai zai iya ba ɗan Adam.”

    Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ƙudurinsa na gina Najeriya ya ƙara ƙarfi, yana mai tabbatar wa ’yan ƙasa cewa zai ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su bunƙasa tattalin arziki, samar da ci gaba da kuma tabbatar da wadata ga al’umma.

    Ya ce: “Ƙudurina na gina Najeriya ya ƙara ƙarfi. Na ƙuduri aniyar kawo wadata da kuma bunƙasa ƙasar nan gaba ɗaya, bisa muradin Allah da goyon bayan al’umma.

    “Yana da muhimmanci a fara da sanya Allah a gaba, sannan a ci gaba. A bi abin da zuciya ta gaskiya take nunawa, a bi hanya madaidaiciya wadda za ta kai Najeriya ga ɗaukaka.”

    Dangane da tattalin arzikin ƙasar, Shugaban ya nuna kyakkyawan fata game da ci gaban da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa, yana mai bayyana cewa an gina tubali mai ƙarfi, kuma ƙasar ta fara fita daga mawuyacin halin da ta shiga.

    Ya ce: “Tushen tattalin arzikin yana da ƙarfi, kuma tattalin arzikin ya fita daga duhun rami. Wannan abin ƙarfafa gwiwa ne.”

    Sai dai ya jaddada cewa gina ƙasa yana buƙatar ci gaba da zuba jari a makomar matasa, yana mai cewa matakan da shugabanni ke ɗauka a yau su ne za su tabbatar da yadda al’umma za ta tuna da su nan gaba.

    Ya ce: “Dole ne mu gina makoma ga matasanmu. Idan ba mu zuba jari a makomarsu ba, ta yaya muke son a tuna da mu a matsayin shugabanni bayan shekaru 50? Wannan shi ne babban abin da ya kamata mu mayar da hankali a kai. Saboda haka, jagorantar ƙasa babbar ni’ima ce.”

    Shugaban ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, faɗaɗa damar samun ci gaba ga matasa, tare da samar da yanayin da zai ba ’yan Najeriya damar cimma burinsu.

    Read also: NITT DG COMMISSIONS NEW SOCIAL CENTRE

    A ƙarshe, ya gode wa Allah bisa damar jagorantar Najeriya, tare da sake tabbatar da ƙudurinsa na tabbatar da amana da jama’a suka ba shi ta hanyar shugabanci mai manufa da jajircewa wajen ci gaban ƙasa.

    A yayin ziyarar, an bayyana cewa Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN; Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Ali Pate; gwamnonin jihohin Borno, Sokoto, Jigawa, Kaduna, Yobe da Kwara; da kuma ’yan kasuwa, ciki har da shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu, da shugaban kamfanin Oando, Wale Tinubu, sun nuna godiyarsu ga Allah da Shugaban Ƙasa bisa damar shiga cikin Ka’aba da yin addu’a tare da shi a wannan wuri mai tsarki na Musulunci.

    FB IMG
    FB IMG 1793606235301
    FB IMG
    FB IMG 1793606230840
    FB IMG
    FB IMG 1793606224623
    FB IMG
    FB IMG 1793606219508
    FB IMG
    FB IMG 1793606214830
    FB IMG
    FB IMG 1793606206888
    FB IMG
    FB IMG 1793606201759
    FB IMG
    FB IMG 1793606242638
    entering kaaba pbat saudi umra
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleDandazon Mata Sun Taru a Kano don jaddada goyon baya ga zaben Shugaba Tinubu a 2027
    Next Article HON. IBRAHIM ABDULLAHI WAIYA THE MOST EXPERIENCED COMMISSIONER WITH NGO AND CIVIL ORGANIZATIONS BACKGROUND THAT PERFORMED EXCELLENTLY AS AN INFORMATION COMMISSIONER BEFORE HIS REDEPLOYMENT TO ANOTHER MINISTRY

    Related Posts

    News

    Gwamna Commends Construction of 13 LCDA Secretariats, Pledges to Consolidate Gains

    November 28, 2026
    News

    Gov Inuwa Yahaya Hails Creative Industry as Platform for Youth Empowerment, Gombe’s Global Visibility

    November 28, 2026
    News

    Gov. Yusuf Commiserates with Yankifi Market Fire Victims in Kano

    November 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026400 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026390 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026274 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026215 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.