Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Dawo da tallafin man fetur zai mayar da Najeriya baya — Mohammed Idris
    News

    Dawo da tallafin man fetur zai mayar da Najeriya baya — Mohammed Idris

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 24, 20264 Mins Read
    FB IMG 1787569597231
    FB IMG 1787569597231

    Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da Najeriya cikin matsalolin tattalin arzikin da ta fuskanta kafin cire tallafin.

    Idris ya ce matakin cire tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka ya taimaka wajen samar da karin albarkatun da aka raba tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

    Read also: NNPC Discount Offers Relief, Does Not Restore Subsidy

    Ya ce a shekarar 2022, Najeriya ta kashe kusan dala biliyan 10 wajen tallafin man fetur, a lokacin da kasar ke fama da raguwar samar da danyen mai da karancin kudaden shiga.

    Ministan ya bayyana cewa bayan cire tallafin, an samu tanadin Naira tiriliyan 15.8 tsakanin watan Yunin 2023 da Disambar 2025, wanda ya kara yawan kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati.

    A cewarsa, daga cikin kudaden, kusan Naira tiriliyan 5.43 sun samu ne ga Gwamnatin Tarayya, yayin da jihohi suka samu Naira tiriliyan 6.52, sannan kananan hukumomi suka samu Naira tiriliyan 3.88.

    Ya ce karin kudaden da jihohi da kananan hukumomi suka samu ya taimaka musu wajen biyan albashi da fansho, tare da kara zuba jari a fannonin kiwon lafiya, ilimi, tituna da sauran ayyukan more rayuwa.

    Idris ya kuma ce karin damar kashe kudi da sauye-sauyen tattalin arzikin suka samar ya taimaka wajen aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da manyan hanyoyi, gidaje, noma, sufuri da tsaro.

    Ya ce sama da gidaje miliyan 10 sun amfana da shirye-shiryen tallafin jin kai, yayin da gwamnatin ta kuma ware sama da Naira biliyan 400 ga wasu manyan shirye-shiryen tallafawa al’umma, ciki har da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND).

    Ministan ya ce sauye-sauyen sun kuma taimaka wajen farfado da kwarin gwiwar masu zuba jari, karuwar kudaden ajiyar waje da kuma habakar samar da danyen mai, wanda ya zarce adadin da kungiyar OPEC ta ware wa Najeriya a wasu lokuta.

    Read also: LET THE RENEWED HOPE STORY BE HEARD: TINUBU’S APPOINTEES FROM THE NORTH MUST TAKE THE MESSAGE TO THE GRASSROOT

    Ya yi gargadin cewa sake dawo da tallafin man fetur a yanzu zai iya kawo cikas ga ci gaban da ake samu a bangaren man fetur, musamman a daidai lokacin da Najeriya ke kara habaka matatun man cikin gida.

    A cewarsa, idan aka koma tsarin tallafin da aka cire, matsalolin karancin man fetur, matsin lamba kan kudaden gwamnati da kuma cin hanci da rashawa da ke tattare da tsarin na iya sake kunno kai.

    Ya ce Najeriya na fuskantar wani nau’in tallafin makamashi a bangaren wutar lantarki, wanda ya lakume Naira tiriliyan 3.14 tsakanin Yunin 2023 da Disambar 2025.

    “Dawo da tallafin man fetur a kan wannan zai kara wa tattalin arzikin kasar wani babban nauyi,” in ji shi.

    Idris ya amince cewa cire tallafin man fetur ya jawo matsin rayuwa ga ‘yan Najeriya, amma ya ce mafita ba ita ce a mayar da tsarin da ya haifar da matsalolin tattalin arziki ba.

    Ya ce abin da ya dace shi ne gwamnati ta kara kokarin ganin amfanin sauye-sauyen tattalin arzikin ya kai ga jama’a ta hanyar samar da ayyukan yi, inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka.

    Ministan ya ce muhawarar dawo da tallafin man fetur ta shafi zabi ne tsakanin ci gaba da amfani da kudaden gwamnati wajen tallafa wa amfani da man fetur ko kuma a karkatar da su zuwa ilimi, kiwon lafiya, tsaro, tituna, wutar lantarki da sauran ayyukan ci gaba.

    Ya kara da cewa kungiyoyin ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki sun yi gargadin cewa sauya manufar gwamnati na iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari tare da yin illa ga dorewar tattalin arzikin kasar.

    Read also: Kano State Government to Construct 50 Houses Along 5km Roads Across 36 Local Government Areas

    “Najeriya ba za ta iya gina tattalin arzikin gobe ta hanyar komawa tsarin tallafin jiya wanda ba ya dorewa ba. Mun wuce wannan tsarin,” in ji Idris.

    Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da kokarin sauya wahalhalun da sauye-sauyen suka haifar zuwa ingantattun ayyukan gwamnati, karin damar tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

    backwards draw returns subsidy us Wii
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Dikko Radda: A Pragmatic Leader Transforming Katsina Through Vision, Commitment and Purpose
    Next Article Asusun Tallafawa Daliban manyan makarantu,NELFUND ya Yabawa Shugaba Tinubu Kan Dorewar Tallafin Lamunin Dalibai

    Related Posts

    News

    COAS DEEPENS MILITARY-TRADITIONAL INSTITUTIONAL PARTNERSHIP FOR NATIONAL SECURITY

    October 9, 2026
    News

    Kano NDC Governorship candidate leaves Nigeria for Lesser Hajj

    October 9, 2026
    News

    Kano State Government to Construct 50 Houses Along 5km Roads Across 36 Local Government Areas

    October 9, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026332 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026253 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026248 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026190 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026176 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026166 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.