Shakka babu Alummar arewacin Nigeria ba Za su taba mantawa da wannan muhimmin aikin ba. An fara aikin a shekarar 2024,Kuma a yau an kusan kammalawa,inda Zai sabunta fatar samun ingantuwar lantarki,da ci gaban Masanaantu,da na ci gaban tattalin arziki.
A ci gaba da dubiyan manyan ayyukan Raya Kasa na Gani Ya Kori Ji da ake aiwatarwa karkashin jagorancin babban Mai Taimakawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fuskar yada labarai da wayar da kan Jamaa Mal Abdulaziz Abdulaziz,inda ayarin maaikatan yada labaran suka dira a wannan muhimiyyar tashar samar da lantarki mai zaman kanta ta Abuja(,AIPP) daya cikin muhimman wuraren samar da lantarki don kyautata jin dadin jamaa.
Shi wannan aikin na samar da lantarki mai zaman kansa na Abuja,yana iya samar da lantarki mai karfin megawatts 1,600,yana da muhimmanci sosai wajen inganta samar da isasshen lantarki,da ake Yi kafada da kafada da aikin Shinfida bututun man gas daga Ajaokuta,zuwa Kaduna zuwa Kano. An tsara wadannan ayyukan ne gaba daya don fadada samar da isasshen lantarki,takwara shi don amfanin jamaa da kanfanoni da Masanaantu,da gidajen dai dai kun jamaa a fadin Kasar nan.
Da ya ke aikin Shinfida bututun gas din ya kusan kammaluwa,shi wannan aikin tashar lantarki na Abuja yana da matukar alaka da aikin,don samar da abubuwan amfani na tattalin arziki da ci gaban Masanaantu Za su matukar amfana da wannan muhimmin aiki na zuba jari.
Kashin farko na aikin samar da tashar lantarkin da zai samar da megawatts 265 na lantarkin ana sa ran kammala shi da hada shi da babban layin lantarki na kasa kafin karshen shekarar nan, tare da kaddamar da kashi na farko layin bututun gas na AKK,wato Ajaokuta zuwa Abuja. Shakka babu wannan muhimmin aikin zai fadada samar da lantarki,da rage yawan matsin lambar da ake samu a babban layin lantarki na kasa,da goyon bayan yunkurin da Kasar nan Ke Yi na samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Yadda Ake aikin ba kama hannun yaro a wajen aikin abin Zakkyau.. An kammala muhimman bangarori na aikin da suka hada wuraren adana kayayyaki,da wuraren ajiye kayayyakin aiki,da tashoshin samar da gas da fetur.da wajen tsabtace ruwa da sauran muhimman bangarori. Bugu da an riga an girke manyan naurori da suka hada da injunan samar da lantarki,da na rarraba lantarkin da sauran su da ke nuni da ke nuni Ko alamta cewa an kusa kammala aikin.
Ana gudanar da wannan aikin ne ta hannun kanfanin man fetur na kasa NNPC,ta hannun reshen kanfanin mai Kula da samar da man gas,inda kuma wani kanfanin Kasar China na aikin injiniya ya ke Kula da tsarin gudanar da aikin..
Ba ya ga inganta samar da lantarki,shi wannan aikin na tashar lantarkin ta Abuja yana samar da guraben aikin yi ga injiniyoyi Yan kasa, masu aikin kere kere,da masu aikin kwadago da sauran maaikata da ke aiki a wajen,suna inganta tattalin arzikinsu da bunkasa tattalin arziki alummar da Ke makwabtaka. Ana fatan cewa idan aka kammala aikin zai samar da infantaccen lantarki ga Masanaantu,da janyo sabbin masu zuba jari,da goyon bayan samar da muhimman abubuwan amfanin jamaa,da ma inganta rayuwar miliyoyin yan Nigeria.
Karin da Za a samu na megawatts 265 a babban layin lantarki na kasa a kashin farko, Shi ma wani abin tarihi ne, a fafutikar da Kasar nan Ke Yi don samun isasshen lantarki,da ci gaban kasa karkashin shirin sabunta fata na wannan gwabnatin.
Saboda haka jamaa a ci gaba da Asduar Allah ya sa wa wannan gwabnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu albarka, daidai lokacin da ta Ke fafutikar sauya yanayin Samar da abubuwan more rayuwar jamaa da Za su amfani mutane wannan zamanin da Yan baya.








