A ci gaba da rangadin ayarin maaikatan yada labarai na Gani Ya Kori Ji, karkashin jagorancin babban Mai Taimakawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Akan yada labarai da wayar da kan Jamaa Mal Abdulaziz Abdulaziz , a wannan Karon sun ziyarci kanfanin samar da Ruwan gas na LNG na kanfanin Greenville da ke Kaduna,don samun cikakken bayanai akan nasarori da tasirin ayyukan da gwabnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi akan jamaa.
Ziyarar ta samar da ma na DA cikakken bayanai na yadda wannan Shirin Ke samun karbuwa a tsakanin masu ababen hawa,da harkokin kasuwanci,da ma sauran alummar kasa. Bisa laakari da yadda ake samun karbuwar amfani da wannan tsarin Na CNG a ababen hawa, yanzun masu ababen hawa da direbobi da masu shiga mota suke jin dadin samun saukin kudin sufuri Idan aka kwatanta da a da Ko kuma amfani da fetur wajen sufuri.
Shi wannan Shirin na mai da ababen hawa masu amfani da ruwan gas, da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bullo da shi, Wani bangare ne na Shirin sabunta fata na wannan gwabnatin,da aka tsara da nufin samarwa Yan Nigeria da tsabtace, kuma hanyar samun makamashi mai sauki don sufuri. Ba ya ga rage kudin zirga zirgar jamaa, Shirin kuma yana samar sababbin kafofin zuba jari,da aamar da aikin yi a fadin wuraren da ake amfani da Fannin CNG,da karfafa guiwan kanfanoni masu zaman kansu su shiga a dama da su wajen samar da abubuwan amfani na makamashi.
A wannan kanfanin na Greenville LNG ,an nuna ma na yadda ake samun karuwar mutanen da ke sauya injunan ababen hawansu daga amfani da fetur,zuwa ruwan man gas,wanda Ke nuni da amannar da Yan Nigeria suka yi wa tsarin. Wannan tsarin ba ma Kawai yana saukakawa jamaa nauyin da ke Kan masu ababen hawa da fasinjoji ne ba,har ma yana taimakawa dorewar kaucewa gurbacewar muhalli,ta hanyar amfani da tsabtacen makamashi,da rage dumamar yanayi.
Nasarar da wannan Shiri na fadar Shugaban kasa CNG ya ke samu na nuni da kyakyawar kudurin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da muhimmai kuma kyawawan sauye sauyen manufofin tattalin arziki,da zai Shinfida ginshikin samun infantaccen lantarki da ci gaba mai dorewa.
A karshe dai shi wannan Shiri na sabunta fata ,sannu a hankali yana haifar da kyakyawan sakamako,kuma Shi wannan Shirin na fadar Shugaban kasa ya Yi fice a matsayin daga cikin Shiri,abin misalin kyakyawar tsarin inganta rayuwar Yan Nigeria,da bunkasa ci gaban tattalin arziki a fadin Kasar nan.


