Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Gwamnatin Tarayya Za ta shiga Wani gagarunin shirin rage kudin sufuri a faɗin Najeriya daga ranar 1 ga Oktoba
    News

    Gwamnatin Tarayya Za ta shiga Wani gagarunin shirin rage kudin sufuri a faɗin Najeriya daga ranar 1 ga Oktoba

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 28, 20263 Mins Read
    FB IMG 1787898173753
    FB IMG 1787898173753

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin tarayya tare da gwamnonin jihohi sun amince da daukar matakan gaggawa domin rage kudin sufuri a fadin ƙasar, musamman ta hanyar amfani da motocin CNG da na lantarki.

    Shugaban ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan ganawarsa da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, inda ya ce gwamnonin sun dauki matakin ne bisa ra’ayinsu domin tabbatar da cewa alfanun sauyin makamashi sun isa ga talakawa.

    Read also: JAGA’S ROUTINE: ENGR JAMIL JAGA JOINS KADUNA POLITICAL LEADERS IN GROUNDBREAKING AND COMMISSIONING MAJOR DEVELOPMENT PROJECTS ACROSS ZARIA AND SOBA LGA.

    Ya ce gwamnatin tarayya ta riga ta zuba jari mai yawa wajen sauya motocin daga amfani da man fetur zuwa ruwa man gas na CNG, inda ya bayyana cewa sama da motoci 120,000 aka riga aka mayar da su zuwa amfani da CNG a fadin Najeriya, yayin da ake shirin samar da wasu kayan sauya fiye da 100,000.

    A cewar Shugaban, ana kuma ci gaba da fadada cibiyoyin sauya motocin zuwa CNG da kuma samar da kayayyakin da ake bukata domin samun CNG a sassa daban-daban na kasar.

    Ya ce ta hannun Midstream and Downstream Gas Infrastructure Fund, gwamnatin tarayya na tallafa wa sama da ayyukan iskar gas 100 a fadin Najeriya, wadanda suka hada da manyan tashoshin CNG 15 da kananan tashoshi 86.

    Shugaban ya ce a watan Mayu ya kaddamar da wasu daga cikin wadannan ayyuka a Legas, Abuja da Owerri, ciki har da cibiyar tashoshin CNG guda 15 a Legas da wata cibiya a Abuja da za ta iya yi wa motoci da kekunan hawa 1,000, da manyan motoci da bas 50 hidima a rana.

    Ya kuma bayyana cewa ya bayar da umarnin kara samar da wasu tashoshin CNG 500 a fadin kasar, baya ga 500 da asusun ya riga ya bayar da umarnin samarwa a farkon shekarar.

    Read also: GROUP PRAYS FOR SPEEDY RECOVERY OF ABDULSALAMI, SEN. MUSA

    Hakan zai kai yawan tashoshin CNG da ake shirin samarwa zuwa 1,000 a fadin Najeriya.

    Shugaban Tinubu ya ce sufuri na cikin gari ne bangaren da ’yan Najeriya suka fi jin tasirin tsadar man fetur, saboda haka jihohi ne ke da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin an sauke kudin sufuri.

    Ya ce gwamnoni sun amince da kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin fara aiwatar da matakan rage kudin sufuri nan take.

    A cewar Shugaban, motar da ke amfani da CNG na iya kashe kashi 60 zuwa 80 cikin 100 kasa da kudin man fetur wajen tafiya.

    Ya ce burin gwamnatin tarayya shi ne daga 1 ga Oktoba, ’yan Najeriya su fara ganin tasirin wannan rangwame ta hanyar saukar kudin sufuri.

    “Mun amince cewa idan man fetur ya yi arha, kudin sufuri ma ya kamata ya yi arha,” in ji Shugaban.

    Read also: Gov. Yusuf Greets Ooni of Ife on 52nd Birthday

    Ya ce matakin na bukatar dukkan matakan gwamnati su ci gaba da yin aiki tare domin tabbatar da an samar da sauki ga ’yan Najeriya.

    Sabuwar Nigeria.

    cng uses fares reduction transport
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGov. Yusuf Condoles Sheikh Abba Koki Over Mother’s Death
    Next Article NIGER STATE GOVERNMENT DETERMINED TO RESCUE KIDNAPPED VICTIMS IN BORGU.

    Related Posts

    News

    GROUP PRAYS FOR SPEEDY RECOVERY OF ABDULSALAMI, SEN. MUSA

    October 18, 2026
    News

    GOBARA TA ƘONE ƊAKUNAN KWANAN ƊALIBAI UKU A MAKARANTAR MAHIYYA GLOBAL ACADEMY DA KE KAURA NAMODA

    October 18, 2026
    News

    JAGA’S ROUTINE: ENGR JAMIL JAGA JOINS KADUNA POLITICAL LEADERS IN GROUNDBREAKING AND COMMISSIONING MAJOR DEVELOPMENT PROJECTS ACROSS ZARIA AND SOBA LGA.

    October 18, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026373 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026344 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026260 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026250 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026194 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026177 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.