Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home»News»“Kashe Malam Masussuka ya saɓa wa ƙa’idojin zaman lafiya da mutunta rayuwar ɗan Adam” – Shugaba Tinubu
    News

    “Kashe Malam Masussuka ya saɓa wa ƙa’idojin zaman lafiya da mutunta rayuwar ɗan Adam” – Shugaba Tinubu

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanOctober 28, 20262 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1793181004077

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar, a garin Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shugaban ƙasar ya kuma umarci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da kamo waɗanda suka aikata kisan domin gurfanar da su a gaban shari’a.

    Read also: PRESIDENT TINUBU CONDEMNS MURDER OF SHEIKH YAHAYA IBRAHIM MASUSSUKA, DIRECTS THOROUGH INVESTIGATION

    A ranar Litinin da yamma ne wasu ’yan bindiga suka kashe malamin da abokinsa a wani harin kwanton-bauna da suka kai musu ta hanyar harbin bindiga daga cikin abin hawa.

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce Shugaba Tinubu ya kaɗu matuƙa da samun labarin kisan.

    Read also: Gov. Radda Leads Delegation on Condolence Visit to Family of Late Sheikh Masussuka

    Sanarwar ta ruwaito shugaban ƙasar yana bayyana kisan a matsayin mummunan aiki da ya saɓa wa ƙa’idojin zaman lafiya da mutunta rayuwar ɗan Adam.

    Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe, mabiyansu, da kuma gwamnatin Jihar Katsina da al’ummarta bisa wannan babban rashi.

    Read also: NIGER STATE GOVERNMENT MOURNS VICTIMS OF FATAL ROAD ACCIDENT, CLARIFIES CIRCUMSTANCES SURROUNDING THE TRAGIC INCIDENT

    Ya kuma umarci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi kan binciken da rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta fara, domin gano waɗanda suka aikata laifin, kama su tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

    Shugaban ƙasar ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma ba iyalansu da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jurewa.

    condemn killing masussuka pbat
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGov. Radda Storms Funtua Zone to Present Building Your Future Scorecard at Tinubu–Dikko Campaign Flag-Off
    Next Article Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Bawa Ma’aikata Tallafin Sufuri na N70,000 Duk Wata

    Related Posts

    News

    Just in: NNPCL to resume exploration in Borno as Zulum meets top management in Maiduguri

    October 28, 2026
    News

    NIGER STATE GOVERNMENT MOURNS VICTIMS OF FATAL ROAD ACCIDENT, CLARIFIES CIRCUMSTANCES SURROUNDING THE TRAGIC INCIDENT

    October 28, 2026
    News

    Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Bawa Ma’aikata Tallafin Sufuri na N70,000 Duk Wata

    October 28, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026385 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026357 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026263 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026253 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026200 Views

    In Katsina State, Bandits Suffer Heavy Casualties as Hunters Repel Attack in Bakori

    October 23, 2026192 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.