Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan tallafin sufuri na N70,000 duk wata ga ma’aikatan gwamnati a dukkan matakan albashi, na tsawon watanni shida, daga watan Nuwamba 2026.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce an cimma matsayar ne a wani taron da aka gudanar ranar Talata tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), domin rage radadin matsin tattalin arziki da ma’aikata ke fuskanta.
Read also: Gov. Radda Pays Condolence Visit to Family of Late Alhaji Tukur Barau
Haka kuma, taron ya amince da fara biyan bashin ‘Peculiar Allowance’ daga watan Nuwamba, wanda aka fara ƙirga wa daga ranar 1 ga Mayun 2026. Za a biya bashin ne kashi uku daidai a cikin watanni uku.
Read also: Gov. Radda Leads Delegation on Condolence Visit to Family of Late Sheikh Masussuka
Bugu da ƙari, ɓangarorin biyu sun amince cewa za a biya ma’aikatan lafiya bashin alawus na watanni 19 cikin watanni uku, daga watan Disamba na 2026.
Taron ya kuma yanke shawarar kafa kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi, wanda zai fara aiki nan take.
Haka kuma, an yi kira ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su shiga cikin shirin tallafin domin faɗaɗa tasirinsa ga ma’aikata.
Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago sun amince da sake zama cikin wata guda domin duba yadda ake aiwatar da yarjejeniyoyin daaka cimma.

