Ibrahim Sani Shawai.
A yayin da siyasar Jihar Gombe ke kara daukar zafi gabanin zabukan da ke tafe, alamomi na nuna cewa sahu ya fara daidaita a fagen takara, inda farin jinin Dokta Jamil Isyaku Gwamna ke ci gaba da karuwa a idon jama’a. Daga birane zuwa karkara, ana ci gaba da jin amon goyon baya daga sassa daban-daban na al’umma, abin da ke kara tabbatar da matsayinsa na mutumin da ake kallon zai iya cire kitse daga wuta idan lokaci ya yi.
Read also: Modernising Katsina at an Unprecedented Pace: Inside Dikko Radda’s Infrastructure Revolution
Karɓuwa da irin goyon bayan da jama’a ke ci gaba da nuna wa Dokta Jamil Isyaku Gwamna daga sassa daban-daban na jihar, hujja ce karara da ke nuna ƙwarewarsa a siyasa, hangen nesansa a harkokin rayuwa, gogewarsa a harkokin gudanarwa da kuma hakurinsa da tawali’unsa na musamman.
Waɗannan kyawawan halaye ne suka sa ya shiga zukatan talakawa, tare da tabbatar da shi a matsayin jagora mai iya haɗa kan al’umma, kare nasarorin dimokuraɗiyya, samar da shugabanci na kowa da kowa da kuma ciyar da muradun al’ummar Jihar Gombe gaba.
Babu shakka, irin ƙaruwar farin jini da ƙarfi da ke tattare da takararsa na nuna irin amincewa da jama’a ke da ita ga shugabancinsa mai cike da hangen nesa. A yau, mutane da dama na kallonsa a matsayin zabin da zai iya sauya akalar ci gaban jihar, musamman ta fuskar tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi ga matasa.
Idan aka yi la’akari da yanayin siyasar da ake ciki a yanzu, da kuma yadda magoya bayan jam’iyyu da masu zaɓe ke ci gaba da nuna ƙwarin guiwa, akwai alamun cewa jam’iyyar APC na kan turbar samun gagarumar nasara mai tarihi a zaɓen da ke tafe a Jihar Gombe.
Read also: ZAMFARA @30: AT LAST, ZAMFARA HAS BEGUN TO FLY
A tsawon shekarun da ya shafe yana mu’amala da jama’a, Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya nuna cikakkiyar ƙwarewa wajen tafiyar da al’amura cikin adalci da gaskiya. Wannan ne ya sa mutane da dama ke kallonsa a matsayin mutum mai cika alƙawari, mai kishin ci gaban al’umma da kuma shugaba da ke da manufar kawo sauyi mai amfani ga rayuwar jama’a.
A yau, matasa, dattawa, mata da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar na ci gaba da bayyana goyon bayansu gare shi, saboda sun yarda cewa yana da abin da ake buƙata domin kai Jihar Gombe zuwa wani matsayi mafi girma na ci gaba da wadata
A ƙarshe, idan aka yi la’akari da irin karɓuwa, kwarewa da kuma hangen nesan da yake da shi, Dokta Jamil Isyaku Gwamna ya bayyana a matsayin jagora da zai iya haɗa kan jama’a tare da kawo cigaba mai ɗorewa. Lokaci ne da al’ummar Gombe za su yanke hukunci, amma alamu sun nuna cewa Jamilu na kowa ya riga ya samu wajen zama a zukatan Al’ummar Jihar Gombe.
Ibrahim Sani Shawai.
14 GA Yuli 2026
Read also: “Tinubu Must Go” Arrests: Don’t Drag Gov. Zulum Into What He Did Not Order

