Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki, zuba jari a ababen more rayuwa da matakan tsaro na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu suna samar da ingantaccen tushe ga bunƙasar tattalin arzikin yankin Arewa ta Tsakiya.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, a wurin taron farko na masu ruwa da tsaki kan cigaban Arewa ta Tsakiya, wanda Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya (NCDC) ta shirya.
Ya ce albarkatun ƙasar noma, ma’adanai, da makamashi sun samar da damarmaki masu yawa na bunƙasa masana’antu, zuba jari da samar da ayyukan yi.
Ministan ya lissafa wasu daga cikin manyan ayyukan ababen more rayuwa da Gwamnatin Tarayya take gudanarwa a yankin, ciki har da gadar Buruku-Logo da hanyar Makurɗi zuwa Gboko a Binuwai, faɗaɗa hanyar Mararaba zuwa Keffi, da babbar hanyar Kalaba zuwa Ebonyi zuwa Binuwai zuwa Nasarawa zuwa Abuja.
Ya ce: “Waɗannan ba hanyoyi da gadoji kawai ba ne; muhimman ababen more rayuwa ne da ke haɗa gonaki da kasuwanni, rage kuɗin sufuri da samar da damarmaki ga kasuwanci da zuba jari.”
Ya kuma ambaci katafaren kamfanin haƙar ma’adinin ‘lithium’ da sarrafa shi na Diamond New Energy, wanda aka zuba jarin dala miliyan 250 a kan sa a Nasarawa, yana mai cewa hakan na nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na sauya yadda ake fitar da ma’adanai daga ƙasa kawai zuwa sarrafa su, bunƙasa masana’antu da ƙara musu daraja.
“Ga Arewa ta Tsakiya, manufar shirin Sabunta Fata ita ce haɗa noma da sarrafa amfanin gona, ma’adanai da masana’antu, makamashi da masana’antu, ƙwarewa da ayyukan yi, da ababen more rayuwa da kasuwanni,” inji shi.
Dangane da tsaro, Idris ya ce Gwamnatin Tarayya tana ƙarfafa Rundunar Soji da ’Yan Sanda ta hanyar ɗaukar ƙarin jami’ai, inganta kayan aiki, amfani da fasaha da bayanan sirri, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, baya ga kafa jami’an tsaron dazuzzuka.
Ya ce kuɓutar da ’yan Nijeriya 308 da aka sace a jihohin Neja da Kwara a watan Agusta yana daga cikin alamun ingantuwar haɗin gwiwar hukumomin tsaro bisa bayanan sirri.
Ministan ya kuma goyi bayan kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa tsarin da aka tsara yadda ya kamata, tare da tanadin da zai tabbatar da ƙwarewa da riƙon amana, zai kusantar da ayyukan ’yan sanda ga al’umma tare da ƙara ƙarfi ga hukumominn tsaron tarayya.
Idris ya buƙaci NCDC da ta mayar da hangen nesan ta na shekaru 20 zuwa ayyukan cigaba da za a iya auna sakamakon su.
“Ba za a auna ‘Babban Tsalle na Ci Gaba’ da yawan tarurrukan da aka gudanar ko takardun da aka samar ba, sai dai da al’ummomin da suka samu ƙarin tsaro, gonaki masu samarwa, ingantattun ababen more rayuwa, sababbin masana’antu, bunƙasar kasuwanci, ayyukan yi ga matasa da kuma ingantuwar rayuwar iyalai,” inji shi.
Da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Tinubu a taron, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya buƙaci NCDC da ta mayar da hankali kan ayyukan da za su kawo sauyi a zahiri tare da rage giɓin cigaba a yankin.
“Ya kamata cigaba ya kasance na al’umma, ba na takarda ba. Bai kamata wannan taro ya zama ɗaya daga cikin tarukan da ake gabatar da ra’ayoyi da samar da rahotanni kawai ba, daga bisani su zama suna taruwa da ƙura a kan ɗakunan ajiya ba,” inji Akume.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NCDC, Dakta Cyril Tsenyil, ya ce manufar taron ita ce sauya tsarin cigaban yankin daga ƙoƙarin kowace jiha daban zuwa tattalin arzikin yanki guda da za a gina bisa ababen more rayuwa, zuba jari da cigaban kowa.
“Babbar tambayar ita ce: Ta yaya za mu sauya wannan dama zuwa kadarori masu amfani, kasuwanci masu gogayya, ayyukan yi masu inganci, da kuma ingantaccen sauyi a rayuwar al’ummar mu da za a iya auna sakamakon sa? Wannan shi ne ƙalubalen wannan taro, kuma shi ya sa aka kafa Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya,” inji Tsenyil.
Sabuwar Nigeria.





