Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaba Bola Ahmed Tinubu Tinubu Ya kalubalanci ‘Yan Adawa: cewa, “Ku ne Silar Jefa Najeriya cikin Yunwa da Talauci”
    Politics

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu Tinubu Ya kalubalanci ‘Yan Adawa: cewa, “Ku ne Silar Jefa Najeriya cikin Yunwa da Talauci”

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanOctober 24, 20263 Mins Read
    FB IMG
    FB IMG 1792869618897

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su sake ba shi damar mulki a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga Janairu, 2027, yana mai alkawarin ci gaba da kawo wadata, daidaito da ci gaba idan aka sake zabensa.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC gabanin babban zaben shekarar 2027.

    Read also: Gov. Radda Gets APC Campaign Flag-Off Banner, Signalling 2027 Governorship Candidacy

    Shugaban ya gode wa al’ummar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, yana mai cewa kuri’unsu sun taimaka masa wajen samun nasarar zama shugaban kasa.

    “Na sake dawowa domin gode muku kan wannan goyon baya, sannan in nemi ku sake ba ni damar mulki a karo na biyu, domin cika alkawarin samar da wadata, ci gaba da samun nasara,” in ji shi.

    Tinubu ya bukaci masu kada kuri’a da su tabbatar sun mallaki katin zabe na (PVC), tare da shiga zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

    Shugaban ya kuma mayar da martani ga ‘yan adawa kan sukar da suke yi wa gwamnati dangane da matsalolin yunwa da talauci, inda ya zarge su da haddasa matsalolin da suke suka a yanzu.

    “Ina jin ‘yan adawa suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne. Su suka haddasa yunwar da talaucin. Mu kuma muna kokarin kawar da su,” in ji Tinubu.

    Ya ce gwamnatinsa na kokarin magance kalubalen da kasar ke fuskanta, yana mai cewa ana biyan albashi a kan lokaci, yayin da gwamnonin jihohi ke aiwatar da shirye-shiryen ci gaba a jihohinsu.

    Read also: GOVERNOR UMARU BAGO IN ATTENDANCE AS PRESIDENT TINUBU FLAGS OFF PRESIDENTIAL CAMPAIGN IN KADUNA

    Tinubu ya bayyana jin dadinsa da ayyukan gwamnonin APC, yana mai cewa yana alfahari da kokarin da suke yi wajen bunkasa jihohinsu.

    Ya kuma soki ‘yan adawa, yana mai cewa fushi da sukar gwamnati ne kawai suke da shi, ba tare da wani abin kirki da za su iya gabatarwa ga al’umma ba.

    Shugaban ya lissafa samar da wadata, daidaito, bunkasa tattalin arziki, farfadowa da samar da damammaki a matsayin wasu daga cikin manufofin gwamnatinsa, tare da gargadin jama’a da kada su yarda a yaudare su da bayanan karya daga abokan hamayyarsa.

    Ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa wannan mataki ya zama tarihi.

    Tinubu ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa, sauya bayanan takardun kudade da safarar kayayyaki ta haramtacciyar hanya, tare da neman karin goyon bayan ‘yan Najeriya.

    Ya bukaci masu kada kuri’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar 16 ga Janairu, 2027, domin zabar APC a dukkan matakan zabe, ciki har da shugaban kasa, gwamnonin jihohi, Sanatoci, ‘yan Majalisar Wakilai da ‘yan majalisun dokokin jihohi.

    Shugaban ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar APC, gwamnoninta da matasa bisa goyon bayan da suke ba shi, yana mai alkawarin samar da kyakkyawar makoma ga ‘yan Najeriya.

    Read also: Zaɓen 2027: Ku manta da maganganun da ake a kafafen sada zumunta, ’yan Najeriya na ƙaunar Shugaba Tinubu – Ministan Yaɗa Labarai

    “Matasanmu, na gode muku. Mun yi muku alkawarin kyakkyawar makoma da gobe mai kyau,” in ji shi.

    Taron na Kaduna shi ne farkon yakin neman zaben shugaban kasa na APC gabanin babban zaben shekarar 2027.

    kd opposition parties pbat thrash
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGOVERNOR UMARU BAGO IN ATTENDANCE AS PRESIDENT TINUBU FLAGS OFF PRESIDENTIAL CAMPAIGN IN KADUNA
    Next Article Zaɓen 2027: Ku manta da maganganun da ake a kafafen sada zumunta, ’yan Najeriya na ƙaunar Shugaba Tinubu – Ministan Yaɗa Labarai

    Related Posts

    Politics

    KADUNA RALLY: ADC MOCKS APC OVER ‘EMPTY SEATS, RENTED CROWD, RECYCLED PROMISES’*

    October 24, 2026
    Politics

    Gov. Yusuf Receives APC Governorship Flag as Kano Takes Centre Stage at Tinubu’s 2027 Campaign Flag-off

    October 24, 2026
    Politics

    Gov. Radda Gets APC Campaign Flag-Off Banner, Signalling 2027 Governorship Candidacy

    October 24, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026381 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026354 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026262 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026253 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026197 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026180 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.