Shugabannin ɗarikar Tijjaniyya daga Najeriya, Aljeriya da Senegal sun kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Wata sanarwar da ta fito daga Fadar Shugaban kasa ta ce Ayarin sun haɗa da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi daga Najeriya, Babban Khalifan Tijjaniyya na Aljeriya, Sheikh Ali Al-Arabi, da kuma fitaccen malamin addinin Musulunci daga Senegal, Sheikh Muhammad Al-Mahy.
Ziyarar ta gudana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda shugabannin suka gana da Shugaba Tinubu.
Sabuwar Nigeria


