Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Abdulaziz Abubakar Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, murnar cika shekaru 58 da haihuwa, a yau Litinin, 28 ga Satumba, 2026.
A cikin saƙon taya murnar, Shugaba Tinubu ya bayyana Sanata Yari a matsayin amintaccen ɗan jam’iyyar APC, gogaggen mai gudanar da mulki kuma jagoran siyasa mai kusanci da al’umma, wanda ƙwarewarsa da iya tsara ayyuka suka taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar da ci gaban ƙasa.
Sanata Yari ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan Jihar Zamfara na tsawon wa’adi biyu, daga shekarar 2011 zuwa 2019. Haka kuma, ya taɓa zama shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, inda ya taka rawa wajen samar da haɗin kai da jagoranci tsakanin takwarorinsa.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba da rawar da Sanata Yari ke takawa a halin yanzu a matsayinsa na Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, inda yake jagorantar ayyukan yaɗa manufofi da nasarorin gwamnatin Tinubu da kuma sauye-sauyen da take aiwatarwa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban ya jinjina wa Sanata Yari bisa jajircewarsa, juriyarsa da kuma ci gaba da riƙe akidun jam’iyyar APC.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Sanata Yari tsawon rai cikin ƙoshin lafiya, hikima da ƙarfi, domin ya ci gaba da yi wa al’ummar da yake wakilta, jam’iyyarsa da ƙasar nanhidima.

