Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, fitaccen dan kasuwa kuma dattijon kasa, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, wanda ya rasu yana da shekaru 90.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin, wanda aka fi sani da Tafidan Adamawa, a matsayin babban jigo da ya taka muhimmiyar rawa a harkokin mulki, siyasa, masana’antu da kasuwanci. Tukur ya taba zama babban manajan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) daga 1975 zuwa 1982, kafin daga bisani ya zama gwamnan tsohuwar Jihar Gongola a shekarar 1983.
Marigayin ya kuma rike mukamin Ministan Masana’antu a gwamnatin Janar Sani Abacha daga 1993 zuwa 1995, sannan ya jagoranci wasu manyan kamfanoni a bangaren masana’antu, noma, sufuri da kasuwanci. A fagen siyasa, ya zama Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa daga watan Maris 2012 zuwa Janairu 2014, yayin da a matakin Afirka ya taka rawa wajen bunkasa kasuwanci da hadin gwiwar tattalin arzikin nahiyar.
Shugaba Tinubu ya bayyana Bamanga Tukur a matsayin mutum mai hangen nesa, karamci da kishin kasa, yana mai cewa Najeriya za ta yi kewar shawarwarinsa da jagorancinsa na uba. Ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, Masarautar Fombina ta Adamawa, gwamnatin da al’ummar Jihar Adamawa da al’ummar kasuwanci da siyasa baki daya, tare da rokon Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya ba shi Aljannar Firdausi, Ya kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.

