Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hori malaman addini da su kara amfani da muryarsu wajen yaki da ayyukan ta’addanci
    Religion

    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hori malaman addini da su kara amfani da muryarsu wajen yaki da ayyukan ta’addanci

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 9, 20262 Mins Read
    FB IMG 1786305108878
    FB IMG 1786305108878

    Sabuwar Nigeria

    Shugaban Ƙasan, ya kuma nemi yi malaman addini a Najeriya, Afirka da sauran sassan duniya da su ci gaba da anfani da muryoyinsu kan yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane, da kuma amfani da addini wajen kashe-kashe da tashin hankali.

    Shugaba Tinubu ya ce babu wata ibada ta gaskiya da za ta samu ci gaba ta hanyar zubar da jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

    Shugaban Ƙasar ya yi wannan horon ne a ranar Lahadi a Kano, a cikin saƙon fatan alheri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya isar a madadinsa a wajen babban Mauludin Shehu Ahmad Al-Tijani (RTA). Ya ce malaman addini na da muhimmiyar gudunmuwar da za su bayar wajen wayar da kan matasa, koyar da zaman lafiya, ilimin addini da kyawawan ɗabi’u, tare da yin kira ga shugabannin siyasa da su yi adalci da nuna tausayi.

    Tinubu ya ce matsalolin da duniya ke fuskanta, da suka haɗa da yaƙe-yaƙe, matsin tattalin arziki, yunwa, ta’addanci da rikice-rikicen da ake haddasawa ta hanyar addini da ƙabilanci, sun ƙara nuna muhimmancin gudunmuwar da shugabannin addini za su bayar wajen wanzar da zaman lafiya.

    Ya ce ɗariƙar Tijjaniyya, saboda yawan mabiyanta da hanyoyin sadarwarta a Afirka ta Yamma da Arewa, ta na da damar taimakawa wajen sasanta rikice-rikice, yaƙi da tsattsauran ra’ayi da jagorantar matasa zuwa tsarkin zuciya.

    Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar muhimmanci ga zaman lafiyar yankin saboda matsayinta a tsakanin kasashen Afirka ta Yamma, da Sahel, da Tafkin Chadi da Tekun Guinea. Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da kare ’yancin ’yan Najeriya na gudanar da addininsu, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da malaman addini da sarakunan gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna.

    Tinubu ya kuma yi ta’aziyyar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya ce rashinsa ya yi matuƙar tasiri a taron, yana mai bayyana shi a matsayin malami, uba kuma mai fafutukar zaman lafiya da kyakkyawar fahimta. Ya ce hanya mafi kyau ta girmama Shehun ita ce a ci gaba da gadon ilimin Alƙur’ani, koyar da kyawawan ɗabi’u, bautar Allah, zaman lafiya da kula da jin daɗin al’ummar da ya bari.

     

    kano prayer tijjaniyya
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Radda Charges Katsina Students to Take Leadership Responsibility
    Next Article Kano Politics: The Rise of Verbal Immorality.

    Related Posts

    Opinion

    Kano Politics: The Rise of Verbal Immorality.

    August 9, 2026
    News

    Gov. Yusuf provides food support for 1,500 newly married couples

    August 9, 2026
    News

    Gov. Yusuf urges 1,500 newlyweds to uphold patience, justice in marriage

    August 9, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026281 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026239 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026218 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026163 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026157 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.