…Ta taya Sanata Jonah Jang Murnar Cika Shekaru 80
SHUGABAR Jam’iyyar Lebo (LP) ta Kasa, Sanata Nenadi Usman, ta yi kira ga shugabannin siyasa da su guji fushi su kuma mayar da zaben 2027 a matsayin gasa ta ra’ayoyi, ba yaki ba.
Usman ta fadi haka ne a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, yayin bikin cika shekaru 80 da haihuwa na tsohon Gwamnan Jihar Filato kuma tsohon Gwamnan Jihar Benue, Sanata Jonah David Jang.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa wanda Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar LP, Ken Asogwa, ya sanya wa hannu a garin Abuja, ranar Asabar.
Asogwa ya ambato shugaban Jam’iyyar yana cewa rayuwar Najeriya ta dogara ne da ko ‘yan siyasa za su iya sanya kasar a sama da muradun jam’iyya da na kashin kansu.
Shugaban Jam’iyyar LP ta yi gargadi game da kalaman batanci kuma ta ce rashin jituwa a siyasa bai kamata ya mayar da ‘yan kasa abokan gaba ba.
Ta ce, “Jam’iyyun siyasarmu na iya bambanta, amma ƙasarmu ɗaya ce. Muna bin tsare-tsare masu zuwa da alhakin gudanar da siyasa ba tare da lalata alaƙar da ke tsakaninmu ba.
Usman ta bayyana Sanata Jang a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda shekarun da ya yi yana aikin soja da dimokuraɗiyya suka sa ya sami matsayi a tarihin Najeriya.
Ta ce aikin Jang ya nuna ladabi, jarumtaka da sadaukarwa, da farko a matsayin jami’in soja, sannan daga baya a matsayin Gwamnan Filato kuma Sanata na Jamhuriyar Tarayya.

