Shugabannin al’ummar Fulani (Ardo Fulbe)
ƙarkashin jagorancin Ardo Aliyu sun nuna goyon baya ga yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Read also: 2027: Uba Sani Rallies Support For Tinubu
Read also: Zaben 2027, Tinubu Ya Kaddamar Da babban Kwamitin Kamfen Dinsa , Ya Bukaci Hadin Kan APC
Read also: President Tinubu Praises Gov. Yusuf’s Symbolic Cap Promoting Renewed Hope Agenda
Shugabannin sun bayyana haka ne yayin ziyarar ban-girma da suka kai ga Darakta-Janar na ƙungiyar Arewa For Asiwaju (A4A), Alhaji Mohammed Badaru Abubakar CON, mni, a ofishinsa da ke Maitama, Abuja, a ranar Laraba.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Ganawar ta mayar da hankali kan batun yadda shugabannin za su bada gudunmawa don sake zaɓen Shugaba Tinubu a babban zaben shekarar 2027.




