Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » 2027: Ƙungiyar Pantamiyya Ta Mara wa Dr. Jamil Gwamna Baya A jihar Gombe, Ta Yi Kira ga Haɗin Kan APC
    Politics

    2027: Ƙungiyar Pantamiyya Ta Mara wa Dr. Jamil Gwamna Baya A jihar Gombe, Ta Yi Kira ga Haɗin Kan APC

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanMay 23, 20263 Mins Read
    FB IMG 1779567745416
    FB IMG 1779567745416

    …Ta ce Gwamna na da karɓuwa a cikin jam’iyya da ma wajen jama’a

    Ƙungiyar Pantamiyya Movement Brothers, ƙarƙashin jagorancin fitaccen mai fafutukar siyasa, Sanusi Hamisu Usman wanda aka fi sani da Ameer Sanusin-Gombe, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dr. Jamil Isyaku Gwamna, gabanin zaɓen 2027.

    Ƙungiyar, wadda ke da Ko’odinatoci Sama da100 a dukkanin Akwatuna na ƙananan hukumomi 11 na jihar, ta ce goyon bayan da ta bai wa Dr. Gwamna ya samo asali ne daga irin karɓuwar da yake samu a cikin jam’iyyar APC da kuma a tsakanin al’umma baki ɗaya.

    Da yake jawabi yayin wata ziyarar goyon baya da suka kai wa Dr. Gwamna, Ameer Sanusin-Gombe ya bayyana ganawar a matsayin mai muhimmanci kuma ta zo a kan lokaci, yana mai cewa ƙungiyar ta kuduri aniyar goyon bayan Dr. Jamil Isyaku Gwamna, wanda zai iya ci gaba da ayyukan ci gaban da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya assasa.

    A cewarsa, gogewar siyasar Dr. Gwamna, kusancinsa da talakawa, da kuma karɓuwarsa a tsakanin ɓangarori daban-daban na jam’iyyar ne suka sa ya zama mafi dacewa da wannan nauyi.

    “Mun zo ne domin nuna goyon bayanmu da jajircewarmu wajen ganin APC ta ci gaba da kasancewa a haɗe tare da samun nasara a 2027. Dr. Gwamna ya nuna tawali’u da kuma ƙwarewar tafiya da kowa,” in ji shi.

    Wannan Na kunshe ne cikin wata sanarwar da Mai taimakawa Dr Jamil Isyaku Gwamna ta fuskar yada labarai, Ibrahim Sani shawai ya rabawa manema labarai.

    Sanusin-Gombe ya kuma yi kira ga tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Farfesa Isa Ali Pantami, da sauran masu neman takara a APC da su haɗa kai da Dr. Gwamna domin amfanin jam’iyya da ci gaban jihar Gombe.

    Ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gagarumar nasara ga APC a zaɓen gwamna da na shugaban ƙasa.

    A nasa ɓangaren, Dr. Gwamna ya gode wa ƙungiyar Pantamiyya bisa fifita haɗin kan jam’iyya fiye da komai, yana mai bayyana ziyarar a matsayin alamar tsaftatacciyar siyasa da jajircewa wajen tabbatar da makomar APC a jihar.

    Dan takarar gwamnan na APC ya tabbatar wa ‘yan jam’iyyar cewa zai rungumi shugabanci mai haɗa kai da kowa, wanda zai ba kowane ɓangare damar da ta dace, don a gudu tare a kuma tsira tare.

    Ya kuma yi kira ga dukkanin tsoffin ‘yan takara da masu ruwa da tsaki da su ajiye bambance-bambancen da suka taso bayan zaɓen fidda gwani, su haɗa kai a matsayin iyali ɗaya domin ci gaba da ayyukan ci gaba da gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ke aiwatarwa.

    Haka kuma, Dr. Gwamna ya sake jaddada aniyarsa ta samar da goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar APC a zaɓen 2027, yana mai cewa haɗin kai da manufa ɗaya su ne ginshiƙan nasarar jam’iyyar a jihar Gombe.

    FB IMG 1779567751425
    FB IMG 1779567751425
    FB IMG 1779567757051
    FB IMG 1779567757051
    FB IMG 1779567765549
    FB IMG 1779567765549
    gwamna Isyaku Pantamiyya sahun tabi
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Fintiri, Fair Primaries and the Rise of a Worthy Successor
    Next Article PANTAMIYYA MOVEMENT THROWS IT WEIGHT BEHIND DR JAMIL ISYAKU GWAMNA,APC GOMBE GUBERNATORIAL CANDIDATE.

    Related Posts

    Politics

    Just In: GOVERNOR UBA SANI OF KADUNA STATE NOMINATES MR JERRY ADAM AS HIS RUNNING MATE FOR 2027 GOVERNORSHIP ELECTION.

    July 28, 2026
    Politics

    ZAMFARA RESCUE MISSION: SENIOR SPECIAL ASSISTANTS RALLY BEHIND GOV. DAUDA LAWAL, PLEDGE TOTAL SUPPORT FOR CONTINUED TRANSFORMATION

    July 28, 2026
    Politics

    Adamawa: Disassociate yourself on plot to replace ADC guber-candidate or face our wrath.. .. Group tells Atiku.

    July 27, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026272 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026235 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026211 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026158 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026155 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026150 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.