Daga Anwar Pantami
Yayin da zaɓukan shekarar 2027 ke ƙara matsowa, siyasar Najeriya na ƙara rikicewa, musamman a bangaren jam’iyyun adawa da ke fama da rashin tabbas da kuma rarrabuwar kawuna. A Jihar Gombe ne wannan matsala ta fi bayyana karara, inda jam’iyyar PDP ke cikin wani mummunan rikici da ya jefa ta cikin shakku kan ko za ta iya tsayawa da ɗan takara guda a zaɓen gwamna.
Tsawon watanni, PDP a Gombe na fama da rikicin shugabanci mai tsanani, wanda ya samo asali daga yadda aka fitar da ɗan takarar gwamna ta wata hanya da ‘yan jam’iyya da dama ke ganin ba ta bi ka’ida ba. Wannan lamari ya ƙara dagula al’amura, musamman ganin cewa jam’iyyar ta dade tana kasa samar da tsayayyen shugabanci mai haɗa kai a jihar.
Abin da ya fi ba wa magoya baya takaici shi ne yadda aka yi watsi da waɗanda suka shafe shekaru suna gina jam’iyyar tun daga tushe, aka maye gurbinsu da wani mutum da ake kallon kamar mai anfani da dama ne kawai. Farfesa Isa Ali Pantami, wanda tarihin sa da alaƙarsa da jam’iyyar ke jefa ayar tambaya kan amincinsa da kuma biyayyarsa ga manufofin PDP.
Sai dai duk wannan cece-kuce ba ta kai girman tambayar da yanzu ke yawo a zukatan al’ummar Gombe ba: Shin PDP tana da sahihin ɗan takarar gwamna na 2027 kuwa?
Wannan tambaya ba wai ta magana ce kawai ba; gaskiya ce da ke neman amsa.
A wani lamari mai ɗaure kai, an ce akwai ɓangarori biyu na PDP a matakin ƙasa da suka bayar da takardun shaidar cin zaɓe ga mutane biyu daban-daban. Wani ɓangare da ake dangantawa da Ministan Babban Birnin Tarayya ya goyi bayan Pantami, yayin da wani ɓangaren kuma da ke ƙarƙashin halastaccen jagoranci na kwamitin Aminu Turaki ya bai wa Hon. Ahmed Yayari takardarsa. Yayari dai gogaggen ɗan siyasa ne, tsohon Shugaban Ma’aikata a gwamnatin Ibrahim Hassan Dankwambo, kuma ya taba zama Ma’ajin Kasa na jam’iyyar.
Wannan abu da bai taba faruwa ba ya jefa magoya bayan jam’iyyar cikin rudani, takaici da rashin kwarin gwiwa. Tsarin ladabi da dimokuraɗiyyar cikin gida da PDP ke alfahari da su sun fara rugujewa a fili.
Illolin wannan rikici suna da girma, kuma suna iya yin tasiri nan gaba. Ba zai yiwu jam’iyya ta shiga zaɓe da ‘yan takara biyu a kujerar guda ba. Wannan ba wai kawai kuskure ba ne, illa ce da za ta iya hallaka jam’iyyar gaba ɗaya.
A wannan lokaci mai muhimmanci, PDP a Gombe na fuskantar barazanar zama ba komai a siyasa. Idan ba a dauki matakan gaggawa ba don sasanta rikicin, haɗa kan ‘yan jam’iyya, da kuma dawo da martabar tsarin ta, akwai yiwuwar jam’iyyar ta shiga zaɓen 2027 cikin rauni ko ma ba tare da ɗan takara ba.
Kuma a siyasa, kamar yadda yake a rayuwa, babu gurbi da yake zama babu mai cikewa.

