Gwamna Inuwa Yahaya Ya Yaba Da Fitowar Dandazon Masu Zaɓe Da Yadda Zaɓen Ya Gudana
…Ya Jaddada Aniyarsa Ta Ƙarfafa Cibiyoyin Demokraɗiyya Da Shugabanci Nagari A Matakin Ƙananan Hukumomi
Jihar Gombe ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli cikin kwanciyar hankali da lumana a dukkanin ƙananan hukumomi 11 dake faɗin jihar
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya baiwa manema labarai.
Sanarwar ta ce an ga yadda masu zaɓe suka fito ƙwansu -da-ƙwarƙwata don sauƙe haƙƙinsu na demokraɗiyya cikin tsari, yayin da jami’an zaɓe dana tsaro suka gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya (CON), wanda ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe ta Yahaya Umaru 010 dake Unguwar Jekadafari a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gombe, ya nuna gamsuwa da yadda zaɓen ya gudana.
Ya kuma yaba da kishin da al’umma suka nuna, tare da nuna gamsuwa da yadda duk masu ruwa da tsaki suka gudanar da lamarin cikin lumana.
Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnatinsa ta himmatu wajen ƙarfafa cibiyoyin demokraɗiyya, da haɓaka tsarin zaɓe ingantacce, da kuma zurfafa shugabanci a matakin ƙananan hukumomi, wanda hakan ginshiƙi ne na samar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Gombe.
“Kamar yadda kuka gani da idanunku, fitowar dandazon jama’a abin burgewa ne. Na riga na kaɗa ƙuri’ata tare da ɗan takaranmu na gwamna a jam’iyyarmu, Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna, da kuma sauran masu zaɓe. Dangane da abin da muka gani zuwa yanzu, zaɓen na tafiya cikin ‘yanci, adalci, da zaman lafiya, kuma na yi imanin cewa sakamakonsa zai zama mai amfani garemu duka,” in ji Gwamnan.
Gwamna Inuwa Yahaya, wanda ya nuna farin cikinsa da yawan fitowar jama’a, yace, “Na ji daɗin kishin da al’ummarmu suka nuna. Fitowarsu cikin lumana shaida ce ta amincewar da suke da ita ga tsarin demokraɗiyya da kuma jagorancinmu.”
Gwamnan ya kuma ce Jihar Gombe ta saba gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi cikin zaman lafiya a tsawon shekaru, inda ya nuna ƙwarin gwiwar cewa, wannan zaɓen ma zai ƙara ƙarfafa martabar demokraɗiyyar jihar.
“Mun sha gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da dama a baya, kuma duk sun gudana cikin zaman lafiya da nasara. Na yi imanin wannan ma zai ƙare lafiya,” inji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa, rahotannin da ya samu daga duk ƙananan hukumomin jihar sun nuna cewa zaɓen ya gudana cikin sauƙi ba tare da wata matsalar tsaro ko wani babban abin damuwa ba.
“Mun gudanar da zaɓe a nan, kuma hakan ne ya faruwa a faɗin jihar. Zuwa yanzu, babu rahoton wata matsala. Nan da sa’o’i kaɗan, za a kammala zaɓe, a fara tattara sakamako, kuma sakamakon zai fito da kyau,” inji shi, yayinda yake ƙira ga ’yan takara su amince da sakamakon zaɓen.
A duk faɗin jihar dai, an lura cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali, tsari, da gaskiya, inda masu zaɓe suka fita don zaɓen waɗanda suke so cikin bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
A rumfunan zaɓe daban-daban, an ga jami’an zaɓe, jami’an tsaro, da masu sanya ido suna gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.
Tuni dai aka tattara sakamakon zaɓen jim kaɗan bayan kammala kaɗa ƙuri’a a duk faɗin jihar.
Wannan shi ne zaɓen farko da aka gudanar tun bayan ƙirƙiro ƙananan hukumomi na wucin gadi (LCDAs) 13 da Gwamna Inuwa Yahaya ya yi, a matsayin wani ɓangare na ƙudurinsa na kusantar da gwamnati ga talakawa da kuma hamzarta kawo ci gaba a matakin ƙananan hukumomi.






