Ibrahim Sani Shawai.
Sardaunan Gombe, Dakta Jamil Isyaku Gwamna mutum ne da a yanzu haka ludayinsa ke kan dawo, bisa la’akari da yadda yake ci gaba da samun karɓuwa a saƙo da lungu na Jihar Gombe.
Karɓuwarsa da irin goyon bayan da jama’a ke ci gaba da nuna wa Dakta Jamil Gwamna, hujja ce ƙarara da ke nuna irin ƙwarewarsa a siyasa, hangen nesansa a harkoki na rayuwa, gogewarsa a harkokin gudanarwa da kuma haƙurinsa da tawali’unsa na musamman.
Waɗannan kyawawan halaye ne suka sa ya shiga zukatan talakawa, tare da tabbatar da shi a matsayin jagora mai iya haɗa kan al’umma, kare nasarorin dimokraɗiyya, samar da shugabanci na kowa da kowa da kuma ciyar da muradun al’ummar Jihar Gombe gaba.
Babu shakka, irin ƙaruwar farin jini da ƙarfi da ke tattare da takararsa ta Gwamna a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC na nuna irin amincewa da jama’a ke da ita ga shugabancinsa mai hangen nesa.
Idan aka yi la’akari da yanayin siyasar da ake ciki a yanzu da kuma yadda magoya bayan jam’iyyu da masu zaɓe ke ci gaba da nuna ƙwarin guiwa, babu ko ja ina da cikakken yaƙinin cewa jam’iyyar APC tana kan turbar samun gagarumar nasara mai tarihi a zaɓen da ke tafe a Jihar Gombe, in sha Allah.
Dakta Jamil, wanda ake wa laƙabi da “Kowa Naka”, mutum ne mai sauƙin kai da son jama’a. Mutum ne da ba shi da abokin faɗa, domin ɗabi’arsa ita ce lumana, hikima da mutunta kowa ba tare da nuna banbanci ba. Ba ya yin magana sai ya yi nazari tare da auna kalamansa cikin natsuwa da basira.
A tsawon shekarun da ya shafe yana aiki, a ɓangare ɗaya kuma da mu’amala da jama’a, ya nuna cikakkiyar ƙwarewa wajen tafiyar da al’amura cikin adalci da gaskiya. Wannan ne ya sa mutane da dama ke kallonsa a matsayin mutum mai cika alƙawari, mai kishin ci gaban al’umma da kuma shugaba da ke da manufar kawo sauyi mai amfani ga rayuwar jama’a.
A yau, matasa, dattawa, mata da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Gombe na ci gaba da bayyana goyon bayansu gare shi, saboda sun yarda cewa yana da abin da ake buƙata domin kai Jihar Gombe zuwa wani matsayi mafi girma na ci gaba mai ma’ana.
Haƙiƙa, idan aka ci gaba da tafiya a kan wannan tsari na haɗin kai, haƙuri da kyakkyawar manufa, babu abin da zai hana Dakta Jamil Isyaku Gwamna samun nasara tare da rubuta sabon tarihin siyasa a Jihar Gombe.

