Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Dan takarar gwabnan jihar Gombe karkashin tutar Janiyyar APC,Dakta Jamil Isyaku Gwamna Ya Buƙaci Al’ummar Gombe: Su Karɓi Katin Zaɓe.
    Politics

    Dan takarar gwabnan jihar Gombe karkashin tutar Janiyyar APC,Dakta Jamil Isyaku Gwamna Ya Buƙaci Al’ummar Gombe: Su Karɓi Katin Zaɓe.

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanJune 5, 20262 Mins Read
    FB IMG 1780668585624
    FB IMG 1780668585624

    Yayin da shirye-shiryen zaɓuka ke ƙara ƙaratowa, fitaccen ɗan siyasa kuma jagoran tafiyar “Gombe Ce a Gabanmu”, Dakta Jamil Isyaku Gwamna, ya buƙaci ɗaukacin al’ummar Jihar Gombe da su tabbatar sun karɓi katin zaɓensu domin su taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar jiharsu.

    A cikin sanarwar manema labarai da Ibrahim Sani shawai mai taimakawa Dr Jamil Isyaku Akan harkokin yada labarai ya ce Dakta Jamil ya bayyana cewa katin zaɓe shi ne ginshiƙin dimokraɗiyya kuma babban makamin da talaka ke da shi wajen tabbatar da an samu shugabanci nagari, adalci da ci gaba mai ɗorewa.

    Ya ce lokaci ya yi da al’ummar Gombe za su nuna kishin jiharsu ta hanyar fitowa domin karɓar katin zaɓensu, ya ce domin babu wani ci gaba da za a samu idan jama’a ba su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe ba.

    “Manufar Gombe Ce a Gabanmu ba ta mutum ɗaya ba ce. Manufa ce ta kowa da kowa; ta matasa, mata, manoma, makiyaya, ma’aikata, malamai, ‘yan kasuwa da dukkan al’ummar jihar Gombe masu burin ganin jiharmu ta samu ci gaba a fannoni daban-daban,” in ji Dakta Jamil.

    Ya ƙara da cewa ci gaban da jama’a ke fata a ɓangarorin ilimi, lafiya, noma, samar da ayyukan yi, kasuwanci da ababen more rayuwa zai samu ne kawai idan al’umma suka kasance cikin masu yanke hukunci ta hanyar amfani da katin zaɓensu.

    Gwamna ya kuma yi kira ga magoya baya da masu ruwa da tsaki a dukkan ƙananan hukumomin jihar da su zama jakadun wayar da kai, su rinƙa ƙarfafa iyalai, abokai da maƙwabta su karɓi katin zaɓensu tare da kiyaye zaman lafiya da mutunta dokokin ƙasa.

    “Muna kira ga kowa da kowa da ya tashi tsaye ya karɓi katin zaɓensa. Katin zaɓe shi ne muryarka, ƙarfinka da makaminka wajen ci gaba da gina Gombe da muke mafarki. Idan muna son Gombe ta kasance ta farko, dole ne mu fara da amfani da haƙƙinmu na zaɓe.” Inji Dokta Gwamna.

    A karshe Dokta Gwamna Ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da dafawa Gwamna Inuwa Yahaya Ya kuma ba al’ummar jihar Gombe haɗin kai, zaman lafiya da hikimar zaɓar shugabannin da za su kai jihar zuwa mataki na gaba.

     

     

    dr gwamna jamil katin zabe
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleTROOPS RECOVER ARMS AND MOTORCYCLES IN SWIFT RAID OPERATION
    Next Article ‎ACTING COMMANDANT NASM EXTOLS NACOLM FOR POSITIVELY SHAPING THE CAREER OF OFFICERS ‎

    Related Posts

    Politics

    Silence Is Complicity: How Peter Obi and Kwankwaso’s Failure to Repudiate Their Supporters’ Insults Against the Sardauna Exposes the True Character of the NDC Ticket.

    June 5, 2026
    Politics

    2027:Adamawa women support group for Tinubu protest Salihu candidacy,begs Ribadu over central senatorial crisis

    June 4, 2026
    Politics

    Why APC Should Look To North Central For Its Vice Presidential Candidate

    June 4, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026226 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026224 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026167 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026138 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026134 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026131 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.