Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka ’yan ta’adda 19 a wasu samame da sintiri da aka gudanar a sassan kasar cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
A jihar Zamfara, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 18 da aka yi garkuwa da su a Sabon Gari, karamar hukumar Kaura Namoda, bayan da suka mayar da martani ga kiran neman agaji, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa. A Jihar Filato kuma, sojoji sun ceto wani mutum da aka sace daga Duguri a Bauchi, yayin da Operation ENDURING PEACE ta hallaka wani dan ta’adda tare da kwato AK-47 da harsasai biyu.
A jihar Kebbi, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka ’yan ta’adda 18 yayin da suka kai hari kan jami’an Mobile Police Special Intervention Squad a Makuku, karamar hukumar Sakaba. Sojojin sun kuma lalata babura biyar tare da kwato bindigogi AK-47 guda biyu kirar gida a wani samame a jihar Filato.
A jihar Borno kuma, dakarun Operation HADIN KAI sun ceto mutane biyar da suka tsere daga wani sansanin ’yan ta’adda a yankin tsaunukan Mandara, bayan rikici ya barke tsakanin ’yan ta’addan. A can jihar Enugu kuwa, sojoji sun kwato AK-47 guda hudu, magazin bakwai da harsasan 7.62mm guda 133 daga maboyar masu garkuwa da mutane a dajin Umuchingu Ujenike.
A jihar Taraba, dakarun sun kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka a karamar hukumar Gashaka, tare da kwato babura, injinan famfo, wayoyin hannu da kudade. Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin kokarin da take yi na amfani da bayanan sirri, sintiri da samame domin dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan Najeriya.
Sabuwar Nigeria.

