Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 25 ga Agustan 2026, a matsayin ranar hutu ta ƙasa domin bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW).
Read also: Gwamnatin Tarayya ta amince da aikin Naira tiriliyan 1.5 na gyaran hanyar Lambata zuwa Kontagora
Read also: Babban Labari,Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin fetur a gidajen NNPCL na wata guda
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, inda ya taya Musulmi a Najeriya da sauran ƙasashen duniya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAWA).
Read also: Kano State Government to Construct 50 Houses Along 5km Roads Across 36 Local Government Areas
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ruwaito Ministan yana cewa Maulidi na ba da damar yin tunani kan darussan da ake samu daga rayuwar Annabi, musamman tausayi da hidima ga sauran mutane, yana mai cewa waɗannan halaye na daga cikin abubuwan da Najeriya ke matuƙar buƙata a yanzu.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da gudanar da bikin cikin natsuwa da mutunta juna. Tunji-Ojo ya tabbatar da aniyar Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

