Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Asusun Tallafawa Manyan Makarantun Kasar Nan,TETFund ta ware N2.53bn ga kowace jami’ar gwamnati a 2026
    Education

    Asusun Tallafawa Manyan Makarantun Kasar Nan,TETFund ta ware N2.53bn ga kowace jami’ar gwamnati a 2026

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 21, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787341043585
    FB IMG 1787341043585

    Gwamnatin Tarayya ta ƙara nuna himmarta wajen farfaɗo da ilimin manyan makarantu, inda Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na Ƙasa (TETFund) ya ware kusan Naira Biliyan 2.53 ga kowace jami’ar gwamnati, Naira Biliyan 1.87 ga kowace kolejojin kimiyya da fasaha,Polytechnic, da Nairan Biliyan 2.06 ga kowace Kwalejin Ilimi a ƙarƙashin shirin tallafin shekarar 2026.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Lokoja yayin taron TETFund na shiyyar Arewa ta Tsakiya.

    Mohammed Idris ya ce tallafin na nuna ƙudirin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙarfafa ilimi da bunƙasa ƙwarewar matasan Najeriya. Ya ce kuɗaɗen za su taimaka wajen ginawa da gyaran ɗakunan karatu da sauran muhimman gine-gine, samar da kayan dakunan gwaje-gwaje, inganta ɗakunan karatu da kuma ƙara tallafa wa bincike da ƙirƙire-ƙirƙire. Ya jaddada cewa gwamnati na kallon ilimi a matsayin muhimmiyar hanya wajen samar da ƙwararrun matasa da za su taimaka wajen gina tattalin arzikin ƙasa.

    Ministan ya kuma ce tallafin TETFund a ƙarƙashin Renewed Hope Agenda ya wuce samar da gine-gine kawai, inda ake ƙara mai da hankali kan fasahar zamani ta Artificial Intelligence, Kwarewar Yanar Gizo, bincike, ƙirƙire-ƙirƙire da horar da ma’aikatan ilimi. Ya buƙaci manyan makarantu su daidaita bincike da shirye-shiryen karatu da buƙatun tattalin arziki, musamman a fannonin noma, ma’adinai, makamashi, masana’antu da fasahar zamani. Ya ce ilimi mai inganci da ƙwarewa na taimakawa wajen rage rashin aikin yi da kuma samar da matasa masu iya taka rawa wajen ci gaban ƙasa.

    A nasa jawabin, Gwamnan Kogi, Ahmed Ododo, ya yaba da ayyukan TETFund wajen bunƙasa manyan makarantu, yana mai kira da a ƙara zuba jari a bincike da ƙirƙire-ƙirƙire. Shi ma mamba a Kwamitin Amintattu na TETFund mai wakiltar Arewa ta Tsakiya, Dakta Abdulrahman Ocholi, ya ce tallafin gwamnatin Tinubu ya haɗa da robotics da coding, 3D printing, makamashi, dakunan binciken AI da biotechnology, mini-grid power projects da innovation hubs. Ya ce hakan na nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke ƙoƙarin sauya manyan makarantu zuwa cibiyoyin samar da ilimi, ƙwarewa da sabbin hanyoyin magance matsalolin ƙasa.

     

    renovation schools tetfund
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleIGP DISU DEPLOYS AIG ZONE 4 TO PLATEAU, ASSESSES BIN’PER ATTACK, REINFORCES SECURITY
    Next Article Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata ranar hutu saboda Maulidin Manzon Rahama

    Related Posts

    Education

    At ABU Sponsio Academica, 14 MBBS best graduating students receive prizes

    August 21, 2026
    Education

    Final-Year Students Begin Practical Application of Skills from Compulsory Skills Development Training

    August 21, 2026
    Education

    Gov Radda Unveils Fresh Support for Outstanding Students, Teachers

    August 20, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026287 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026221 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026158 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.