Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Yadda Matakan Gyaran da Tinubu ya bullo da su,Suka Kawo Ƙarshen Matsalar Biyan Albashi A Jihohi 27
    News

    Yadda Matakan Gyaran da Tinubu ya bullo da su,Suka Kawo Ƙarshen Matsalar Biyan Albashi A Jihohi 27

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 21, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787340971833
    FB IMG 1787340971833

    A watan Mayun 2023, lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara aiki, jihohi 27 daga cikin 36 na Najeriya na fuskantar matsalar biyan albashin ma’aikatansu, yadda ya kamata. Shekaru uku bayan haka, wannan adadi ya sauya, babu wata jiha da take kasa biyan albashin ma’aikatan ta a cewar alkaluman da gwamnatin tarayya ta gabatar a cikin “Nigeria’s Reform Scorecard”.

    Wannan sauyi na zuwa ne bayan wasu manyan sauye sauyen tattalin arziki da suka hada da cire tallafin man fetur da sake fasalin tsarin canjin kudaden waje. Tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025, an samu Naira tiriliyan 15.8 na tanadin kudaden tallafin man fetur, inda aka raba wa jihohi da kananan hukumomi Naira tiriliyan 10.4.

    Read also: OPEN LETTER TO HIS EXCELLENCY, MR. PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU, GCFR PRESIDENT AND COMMANDER-IN-CHIEF OF THE FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA

    Read also: Another Milestone: Gov Inuwa Yahaya Flags Off N10.32bn Gratuity Payment to 6,665 State, LG Retirees

    Karin kudaden da jihohi suka samu ya kara musu azamar gudanar da ayyukansu, ciki har da biyan albashi da kuma daukar nauyin ayyukan ci gaba. A matakin tarayya kuma, an ware Naira tiriliyan 9.39 domin karin albashi, sabon mafi karancin albashi da alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati.

    Read also: PRESIDENT TINUBU CONGRATULATES GOVERNOR INUWA YAHAYA ON HIS 65TH BIRTHDAY

    Wannan ya kuma taimaka wajen samun karin albarkatun da suka bai wa gwamnati damar kara mafi karancin albashi daga Naira 30,000 zuwa Naira 70,000. Bayanai irin wadannan na nuna cewa gyaran tattalin arziki ba ya tsaya kan alkaluman gwamnati kadai ba, yana shafi ma’aikata da iyalansu kai tsaye.

    Duk da cewa har yanzu akwai kalubalen tsadar rayuwa da bukatar kara inganta jin dadin jama’a, sauyi daga jihohi 27 masu fama da matsalar albashi zuwa yanzu da babu wata jiha da ke da wannan kalubalen na daga cikin muhimman alamomin da ke nuna kokarin sake gina tsarin tattalin arzikin Najeriya. Gyaran ya fara samar da daidaito, babban aikin yanzu shi ne tabbatar da amfaninsa ya isa ga talaka.

    economic payment reforms salaries
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGwamnatin Tarayya ta ayyana Talata ranar hutu saboda Maulidin Manzon Rahama
    Next Article Rundunar’Yan sanda ta kubutar da mutane 75 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

    Related Posts

    News

    NNPC Discount Offers Relief, Does Not Restore Subsidy

    October 9, 2026
    News

    JAGA’S ROUTINE: CHAIRMAN JAGA PRESIDES OVER 19TH EXECUTIVE COUNCIL MEETING, RECEIVES NIPSS DELEGATION ON STRATEGIC ASSESSMENT.

    October 9, 2026
    News

    PRESIDENT TINUBU CONGRATULATES GOVERNOR INUWA YAHAYA ON HIS 65TH BIRTHDAY

    October 9, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026331 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026252 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026248 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026190 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026176 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026166 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.