Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » An Bude Babban Taron Maaikatan Yada Labarai Na Arewacin Kasar Nan ,inda aka hore su tsaya Akan kaidojojin aikinsu da kyautata alakar gwabnati da Alumma.
    News

    An Bude Babban Taron Maaikatan Yada Labarai Na Arewacin Kasar Nan ,inda aka hore su tsaya Akan kaidojojin aikinsu da kyautata alakar gwabnati da Alumma.

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanJuly 6, 20264 Mins Read
    FB IMG 1783368207621
    FB IMG 1783368207621

    Sabuwar Nigeria.

    Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga maaikatan kafafen yada labarai su riƙa tantance gaskiyar bayanai kafin wallafawa Ko sanar da jamaa.

    Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Abdulaziz Abdulaziz, Shi ne ya gabatar DA wannan bukatar wajen wani muhimmin taron yada labarai da aka yi a kano.

    Abdulaziz Abdulaziz ya ce bunƙasar dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa muhimmin alamari be da Ke bukatar amincewa da Samun haɗin kai a tsakanin gwamnati, da kafafen yaɗa labarai da kuma al’umma.

    Babban Mai Taimakawa Shugaban kasan ya bayyana cewa tilas ne kafofin yada au rika laakari da yanayin kasa da sa ra ana duban bakin gatari a ayyukan da suke Yi din amfanin zaman lafiya da walwala da kuma ci gaban kasa.

    A cewarsa taron ya haɗa shugabanni, ‘yan jarida, masu ƙirƙirar Ko rubuta abubuwan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, masu tasiri da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a ƙarfafa alaƙar gwamnati da jama’a ta hanyar gaskiya, riƙon amana da ɗabi’ar aikin jarida.

    Abdulaziz Abdulaziz ya ce taron da aka Yi wa taken “ Yarjejeniya a tsakanin alumma da gwabnatin, kamanta gaskiya,nauyin da ya rataya a wuyar gwabnati da Yan jarida,da kuma tsarin gudanar da aikin jarida “,wato “Government-Citizen Accord: Accountability, Responsibility and Ethical Media Practice” ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sake samun kyakyawan Alaska da amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.

    Ya bayyana cewa gwamnati na da alhakin buɗe ƙofofin samun bayanai, yayin da al’umma ke da nauyin tabbatar da gaskiya kafin yaɗa bayanai da kuma riƙe gwamnati da alhakin ayyukanta cikin lumana.

    Ya ce kafafen yaɗa labarai tankar tsani be a tsakanin gwamnati da jama’a, yana mai cewa ingantaccen aikin jarida da tabbatar da sahihancin labarai na taimakawa wajen samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

    Abdulaziz ya kuma jaddada cewa masu tasiri a shafukan sada zumunta sun zama sabbin masu jan ragamar yaɗa bayanai, don haka wajibi ne su riƙa tantance gaskiyar bayanai kafin wallafawa.

    “A yau, saƙon da aka wallafa na iya haifar da fata ko kuma tayar da husuma cikin ɗan lokaci. Don haka bai kamata neman farin jini ko yawan masu kallo ya zama sanadin jefa ƙasa cikin rikici ba,” Kamar yadda ya ce.

    Ya ƙara da cewa yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙaratowa, akwai buƙatar masu amfani da shafukan sada zumunta Na zamani su ɗauki kansu a matsayin masu tabbatar da zaman lafiyar al’umma, tare da gyara kura-kurensu idan sun faru.

    Ya bayyana cewa a wani ɓangare na shirye-shiryen taron, an horas da sama da mutum 100 daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dabarun yaɗa bayanai da bayyana manufofi da nasarorin gwamnati yadda ya kamata.

    Haka kuma ya ce an ƙaddamar da shirin Gani-Ya-Kori-Ji, wanda zai zagaya jihohin Arewacin Najeriya domin duba da kuma haska ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suka aiwatar, musamman waɗanda jamaa ba su San da su ba.

    Abdulaziz ya ce taron ya nuna irin ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare ‘yancin faɗin albarkacin baki, ƙarfafa tattaunawa da kuma bunƙasa dimokuraɗiyya.

    Ya bayyana cewa an tsara taron ne domin bai wabma su mabambantan ra’ayoyi da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya damar tattaunawa kan makomar hulɗar gwamnati da jama’a.

    A ƙarshe, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da karɓar baƙuncin taron, yana mai cewa Kano ta ci gaba da kasancewa cibiyar siyasa, kasuwanci da tattaunawa a Najeriya

    Ya buƙaci mahalarta taron su fito da sabbin dabarun da za su inganta tsarin gudanar da mulki a bayyane, da ƙarfafa ɗabi’ar aikin jarida da kuma inganta alaƙar gwamnati da al’umma.

    FB IMG 1783368175739
    FB IMG 1783368175739
    FB IMG 1783368162833
    FB IMG 1783368162833
    FB IMG 1783368156971
    FB IMG 1783368156971
    FB IMG 1783368149911
    FB IMG 1783368149911

     

     

    babban kano labarai maaikatan taron yada
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleSpeaker Abbas announces 3rd NASS Open Week to hold July 14 – 16
    Next Article NIGER STATE GOVERNMENT VISITS RAFI COMMUNITIES, DIRECTS SECURITY ARCHITECTURE TO CURB BREAKDOWN OF LAW AND ORDER.

    Related Posts

    News

    Governor Inuwa Yahaya Constitutes Panel to Probe Allegations of Misconduct Against Acting Director of Public Prosecutions

    August 1, 2026
    News

    CCE STRESSES INTEGRITY, SAFETY, AND PROFESSIONAL EXCELLENCE AT COMBINED NIGERIAN ARMY ENGINEERS VIRTUAL CONFERENCE 2026

    July 31, 2026
    News

    Yobe Gather For Barr. Umar Ibrahim Gaidam and Asma’u In Abuja

    July 31, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026276 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026235 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026213 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026159 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026156 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.