Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon kokari da aiki tukuru ga al’ummar Jihar Kaduna da arewacin Najeriya yasa mai girma Sarkin Badarawa Alhaji Amadu Dahiru,da ke cikin garin Kaduna ya nada shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman a matsayin Sardaunan Badarawa Kaduna.
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman dai haifaffen unguwar Badarawa ne nan ya tashi kuma a nan ya yi karatunsa na Firamare, sakandare da sauran karatunsa na addinin Musulunci.
An dai yi wannan babban taron nadin ne a harabar ofishin Sarkin Badarawa Kaduna inda dimbin jama’a da dama suka taru domin taya al’ummar da aka yi wa nadin murna.
Da yake gabatar da jawabi jim kadan bayan kammala nadin dukkan wadanda aka naɗa a masarautar ta Badarawa, Talban Badarawa cewa ya yi dalilin da yasa aka yi wa jama’ar nadin an yi ne bisa cancanta.
“An yi maku wannan nadin ne bisa cancanta sakamakon wadansu bayanan da aka samu daga wurin wadansu mutane da masarautar ta yi dogaro da su”.
Shi ya sa Sarkin Badarawa da Majalisar sa suka ga dacewar hakan, saboda haka kada wai nauyin da aka dora maka ya zama wata hanya ta biyan buƙatar kashin kai.
Duk inda kuka je ku wakilan Sarkin Badarawa ne da jama’ar Badarawa don haka zaku kare mutunci da da’arku da taimakon da kuke yi wa al’umma duk su suka tattara suka sanya aka ba ku wannan sarautar.
Allah ya sa wannan nadin ya zama wata sila ce ta ci gaba domin komai ya na da dalilai.
Bayan kammala jawabai da kade kade da bushe bushe irin na sarauta kamar yadda sarautar ta gada a wajen taron sai Marafan Badarawa Kwamared Ayuba Magaji Suleiman shugaban kungiyar Kwadago na Jihar Kaduna ya yi jawabin godiya a madadin dukkan sauran wadanda aka naɗa a wurin taron.
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman ya kuma yi wa Sarkin Badarawa da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli godiya da wannan karancin da suka yi masu na nadin Sarautu daban daban.
Ya kuma yi alkawarin cewa lallai za su ci gaba da yin biyayya sau da kafa a koda yaushe ba tare da gajiya wa ba.
” Muna tabbatarwa da Sarki cewa a koda yaushe za a same mu masu biyayya ga masarauta da kuma rungumar ayyukan jama’a baki daya ba tare da gajiyawaba in Allah yaso”.

