Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Dakta Jamil Gwamna (Sardaunan Gombe), ya sake jaddada ƙudirinsa na ganin ya hada kan al’umma guri guda don ƙara haɓaka ci gaban Jihar.
Dakta Gwamna ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatinsa da yardar Allah za ta kasance mai kula da jama’a tare da bai wa kowa dama, inda babu wanda za a bari a baya saboda asali, jinsi ko matsayinsa a cikin al’umma.
Wata sanarwar da Mai taimakawa Dr Jamil Isyaku Gwamna Akan harkokin yada labarai Ibrahim Sani Shawai ya bayar, ya ce Dr Jamil Isyaku Gwamna Ya yi alƙawarin samar da gwamnati inda kowace murya za ta kasance mai muhimmanci kuma kowane ɗan ƙasa zai taka rawa a harkokin mulki daidai da matsayinsa.
Sardaunan Gombe ya kuma miƙa hannu na neman haɗin kai ga sauran masu neman takara don a kasance tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya. Dakta. Gwamna ya bayyana su a matsayin abokan tafiya wajen ci gaba maimakon abokan takara.
Ya ce, “Dukkanmu muna da manufa guda ɗaya, wato ci-gaban Jihar Gombe. Ina miƙa hannun haɗin kai ga dukkan masu neman takara, don mu gudu tare mu kuma tsira tare.
A ɗaya ɓangaren, Gwamna ya yaba wa nasarorin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, yana mai cewa gwamnatinsa ta kafa tubali mai ƙarfi na ci-gaba a fannoni daban-daban na rayuwa.
Ya jaddada cewa shugabancinsa zai mayar da hankali wajen ƙarfafa waɗannan nasarori tare da hanzarta ci-gaba a fannoni masu muhimmanci kamar ilimi, lafiya, gina ɗan Adam, gine-gine, noma da ƙarfafa matasa.
Dakta Gwamna ya kuma sake tabbatar da ƙudirinsa na daidaita Jihar Gombe da Ajandar “Sabunta Fata” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’ummar Jihar Gombe baki ɗaya.
Ɗan takarar APCn ya yi alƙawarin kafa gwamnati mai sauraron al’umma da aiki tuƙuru da kuma samar da sakamako na zahiri ga jama’a.
A ƙarshe Dakta Gwamna ya yi kira ga al’ummar Jihar Gombe da su rungumi haɗin kai, ci-gaba da shugabanci nagari.
“Wannan shi ne lokacinmu na zaɓar haɗin kai maimakon rarrabuwar kawuna, ci-gaba maimakon siyasa da shugabancin da zai yi wa jama’a aiki na gaskiya.”

