Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Dokta Jamil Isyaku Gwamna, ya bayyana aniyarsa ta zagaya dukkan ƙananan hukumomin jihar domin neman kuri’ar al’umma kai tsaye, duk da irin gagarumin goyon bayan da yake samu daga sassa daban-daban na jama’a a faɗin jihar.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Ibrahim Sani Shawai,mai taimakawa Dr Jamil Isyaku Gwamna ta fuskar yada labarai ya baiwa manema labarai.
Sanarwar ta ce Dr. Gwamna ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Gombe, inda ya jaddada cewa dimokuraɗiyya na buƙatar kusanci da jama’a da kuma neman amincewarsu kai tsaye.
Ya ce, duk da cewa ya na samun cikakken goyon baya daga yan jam’iyyun adawa, ‘yan kasuwa, ‘Kungiyoyi, malamai da sauran masu ruwa da tsaki, hakan ba zai hana shi sauka ƙasa domin ci gaba da tuntuɓar al’umma ba, domin a cewarsa, neman kuri’a daga bakin jama’a shi ne ginshiƙin nasara mai ɗorewa.
“Duk da irin tarin goyon bayan da nake samu daga bangarori daban-daban, hakan ba zai sa na zauna ba. Zan shiga lungu da sako a duk faɗin jihar Gombe domin ganawa da al’umma, sauraron damuwarsu, da kuma neman amincewarsu da kuma kuri’arsu,” in ji Dokta Gwamna.
Ya kuma tabbatar da cewa zai gudanar da yaƙin neman zaɓensa cikin tsafta, lumana da mutunta juna, tare da mai da hankali kan manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar Jihar Gombe gaba ɗaya.
Dokta Gwamna ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba shi goyon baya tare da fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin amfani da haƙƙinsu na zaɓe a lokacin da ya dace, yana mai jaddada aniyarsa ta kawo ci gaba mai ma’ana idan aka ba shi dama ya jagoranci jihar.
A karshe Dokta Jamil Gwamna ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON Kan Irin ci gaban daya kawo a fannoni daban- daban na rayuwa a Jihar Gombe, tare da alkawarin ci gaba daga inda ya tsaya.

