Sabuwar Nigeria.
A ci gaba da rangadin manyan ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Ke gudanarwa a Jihar Kano a ƙarƙashin shirin Arewa Media Summit, ayarin masu yaɗa labarai sun kai ziyara zuwa aikin hanyar Bayan Gari da Ake ginawa a arewacin Kano (Northern Bypass,) wanda ake sa ran zai sauya fasalin zirga-zirga da harkokin kasuwanci a jihar.
Rangadin, wanda Ofishin Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya shirya, na da nufin bai wa mahalarta taron cikakken haske da Kuma Gani da Ido kan muhimman ayyukan gwamnatin tarayya da ke gudana a Arewacin Najeriya.
Aikin Kano Northern Bypass, mai tsawon kusan kilomita 38, ya taso ne daga kan hanyar Kano zuwa Hadejia zuwa hanyar Kano zuwa Katsina, inda ake sa ran zai rage cunkoson manyan motoci da ke ratsawa cikin birnin Kano.
Masana sun bayyana cewa idan aka kammala aikin, zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki da fasinjoji, rage bata lokacin da Ake Yi a hanyoyin shiga kano da kuɗaɗen sufuri, tare da bunƙasa harkokin masana’antu da kasuwanci a yankunan da hanyar ta ratsa.
Haka kuma, ana sa ran aikin zai ƙara jawo sabbin masu zuba jari da samar da ayyukan yi ga matasa, musamman a yankunan Zaura, Dawanau, Tarda da sauran al’ummomin da ke kusa da hanyar.
Shugabannin shirin Arewa Media Summit sun bayyana cewa rangadin na da muhimmanci wajen bai wa ‘yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta damar gani da ido da kuma fahimtar irin ci gaban da ake samu a ƙarƙashin Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Tinubu.
Sun ce samar da sahihan bayanai da rahotanni ma su dogaro da hujjoji za su taimaka matuka wajen ƙarfafa fahimtar jama’a game da ayyukan raya ƙasa da ake aiwatarwa a yankin Arewa da ma Najeriya baki ɗaya.
Ana sa ran taron Arewa Media Summit da za a gudanar a ranar 6 ga watan Yuli, 2026, a Coronation Hall da ke Fadar Gwamnatin Jihar Kano, zai haɗa manyan ‘yan jarida, masu tasiri, masana da masu ruwa da tsaki domin tattauna gudunmuwar da kafafen yaɗa labarai Za su bayar wajen bunƙasa ci gaban Arewa.







