Sabuwar Nigeria.
A ci gaba da rangadin ‘Gani Ya Kori Ji’ na manyan ayyukan gwamnatin tarayya a Arewacin Najeriya, Ayarin yan jarida da ke rangadi tare da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, sun kai ziyara aikin gina layin dogo na zamani na da ya tashi daga Kano–Maradi domin duba yadda aikin ke gudana tare da samun cikakken bayani daga jami’an da ke kula da shi.
A yayin ziyarar, Manajan Wurin Aikin ya bayyana wa ayarin cewa aikin na tafiya yadda aka tsara, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa idan aka ci gaba da aiki a wannan mataki, ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen shekarar nan.
Ya ce layin dogon na daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka tsara domin inganta hanyoyin sufuri, bunƙasa kasuwanci da haɗa tattalin arzikin Najeriya da na Jamhuriyar Nijar.
An bayyana wa mahalarta rangadin cewa babban layin dogon zai tashi daga Kano zuwa Maradi mai tsawon kusan kilomita 285, yayin da wani reshe mai tsawon kusan kilomita 108 zai haɗa Kano da Dutse a Jihar Jigawa. Da zarar an kammala aikin, zai sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki, rage cunkoson manyan tituna, da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar tare da buɗe sabbin damarmaki ga jihohin Kano, Jigawa, Katsina da sauran yankunan da ke makwabtaka da su.
Jami’an aikin sun kuma bayyana cewa layin dogon zai haifar da dubban guraben ayyukan yi kai tsaye da kuma a fakaice ga injiniyoyi, masu sana’o’in hannu, ma’aikatan sufuri, ‘yan kasuwa, kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki. Haka kuma, zai ƙara ƙarfafa masana’antu, jawo masu zuba jari, bunƙasa darajar noma tare da bai wa manoma damar kai amfaninsu cikin sauƙi zuwa manyan kasuwanni.
Masu aikin jaridar da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ sun bayyana cewa irin wannan rangadi na ba su damar gani da ido kan yadda manyan ayyukan gwamnatin tarayya ke gudana maimakon dogaro da jita-jita. Sun ce aikin layin dogo na Kano–Maradi wata muhimmiyar shaida ce ta ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta hanyar gina ingantattun ababen more rayuwa, ƙarfafa haɗin kan yankuna da bunƙasa tattalin arzikin Arewacin Najeriya da ƙasar baki ɗaya.





