Sabuwar Nigeria.
Ayarin shirin “Gani Ya Kori Ji” ƙarƙashin jagorancin Babban Mai taimakawa Shugaban kasa na Musamman ga kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Abdulaziz Abdulaziz, sun ci gaba da rangadin duba manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar ta biyu da ziyarar wasu manyan ayyuka a Jihar Kano.
Shirin, wanda aka ƙaddamar domin bai wa ’yan Najeriya damar gani da idanunsu irin ayyukan da Shirin Renewed Hope da gwabnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, na nufin duba, sa ido da kuma tantance ayyukan da aka kammala da kuma waɗanda ake ci gaba da yi, maimakon dogaro da shaci fadi Kawai..
A ranar farko ta Ziyarar, ayarin sun isa Aikin noman rani na Challawa da ke Ƙaramar Hukumar Karaye, inda suka duba yadda aikin ke gudana da kuma irin gudummawar da ake sa ran zai bayar wajen bunƙasa noma da samar da wadataccen abinci.
Daga nan Kuma Ayarin zakakuran manema labaran zarce zuwa Renewed Hope City da ke Janguza a Kano, inda suka zagaya kashi na farko da na biyu na aikin gidajen gwamnatin tarayya.
Wannan aikin yana daga cikin manyan shirye-shiryen gwamnatin tarayya na samar da gidaje masu inganci da sauki domin rage ƙarancin gidaje a ƙasar, tare da samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arziki.
Rahotanni sun nuna cewa aikin ya ƙunshi fiye da gidaje 1,000. An kammala Kashi na farko da ya ƙunshi gidaje 325, waɗanda ke jiran ƙaddamarwa, yayin da ake ci gaba da aikin kashi na biyu wanda zai ƙara kusan gidaje 698.
Aikin ya ƙunshi gidaje iri-iri domin biyan bukatun iyalai daban-daban, ciki har da rukunin gidaje bene da na ƙasa masu dakuna uku,you, da huɗu , hudu da kuma masu dakuna biyar, biyar.
Jagoran ayarin Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ce shirin “Gani Ya Kori Ji” zai ci gaba da kai ziyara zuwa wasu manyan ayyukan gwamnatin tarayya a jihohin Arewacin Najeriya domin bai wa jama’a damar ganin ci gaban da ake samu ƙarƙashin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da gaskiya da bayyana ayyukan gwamnati kai tsaye ga al’umma ta hanyar kai su wuraren da ake aiwatar da su domin su gani da idanunsu da Kuma kararwa ga jamaa.







