Sabuwar Nigeria.
A ci gaba da dubiyan manyan ayyukan Raya Kasa da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a arewacin Kasar nan, a wannan Karon Ayarin sun Duba aikin hanyar bayan garin Kaduna ta arewacin birnin da ake Yi.
Ayarin maaikatan yada labaran sun isa wajen aikin ne, karkashin jagorancin babban Mai Taimakawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu,ta fuskar yada labarai da wayar da kan Jamaa, Mal Abdulaziz Abdulaziz.
Shi wannan aikin hanyar bayan garin Kaduna ta arewacin birnin,yana daga cikin muhimman ayyukan Raya da ake Yi don inganta zirga zirga,da rage cunkoson ababen Hawa da bunkasa tattalin arziki da walwalare alummar jihar Kaduna da arewacin Kasar nan gaba daya.
Duk da cewa an amince a fara aikin hanyar a shekarar 2021, amma ba a fara aikin a lokacin ba, saboda matsaloli da dama. Sai dai kuma bayan hawane Shugaba Bola Ahmed Tinubu akan karagar mulki a shekarar 2923, an sami tagomashin fara aikin gadan gadan karkashin shirin sabunta fata na wannan gwabnatin.
Idan aka kammala aikin hanyar bayan garin Kaduna ta arewacin birnin,zai taimaka ga ya wajen rage tsawon lokacin da ake dauka da masu ababen hawa Ke dauka,da karkatar da manyan motocin dakon kaya daga bin hanyoyin cikin birni,da maganin faruwan hadarurruka da saukaka zirga zirgar jamaa da kayayyaki. Haka kuma aikin ya samar da guraben aikin yi ga injiniyoyi Yan kasa,da masu aikin kwadago,da sauran maaikatan da ke aiki a wannan hanyar da ake ginawa,da kuma yaukaka fannonin tattalin arziki na aummomin da ke kusa DA wajen aikin.
Da yardar Allah ana sa ran kammala aikin hanyar nan da watan Disamba 2026, wanda hakan Na nuna kyakyawar aniyar gwabnatin tarayya na zamantar da muhimman abubuwan more rayuwar jamaa a fadin arewacin Kasar nan don jin dadinsu.
Shakka babu Alumma arewacin Kasar nan ganau ne na irin garabasar da Shirin nan Na Shugaba Bola Ahmed Tinubu,na sabunta fata Ke samarwa,inda ayyukan Raya Kasa da dama,da a baya suke tafiyar hawainiya, amma yanzun kuma Ake samun ci gaba yadda ya kamata.










