Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Tsohon Ministan Kuɗi, Sardaunan Sakkwato, Alhaji Alhaji
    News

    Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Tsohon Ministan Kuɗi, Sardaunan Sakkwato, Alhaji Alhaji

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanJuly 31, 20262 Mins Read
    IMG 20260730 WA0018
    IMG 20260730 WA0018

    Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya (NNGF) ta bayyana matuƙar baƙin cikinta game da rasuwar tsohon Ministan Kuɗi kuma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji, wanda ya rasu a safiyar jiya Alhamis a Abuja.

    A cikin wani saƙon ta’aziyya, Shugaban Ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya bayyana marigayi Alhaji Abubakar Alhaji a matsayin ƙwararren ma’aikacin gwamnati kuma dattijo mai ƙima, wanda ya ba da gudummawa ta fannoni daban-daban don ci gaban ƙasa a shekaru da dama da ya shafe yana hidima cikin gaskiya da amana.

    Ya tuno cewa Alhaji Abubakar Alhaji ya riƙe manyan muƙamai, ciki har da Ministan Tsare-tsare na Ƙasa sannan daga baya ya zama Ministan Kuɗi a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tattalin arzikin ƙasar nan. 

    Baya ga aikinsa na minista, an naɗa shi Babban Jakadan Najeriya a Birtaniya a shekarar 1992, muƙamin da ya riƙe tare da yiwa Najeriya hidima da cikakkiyar girmamawa.

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin na Arewan ya kuma yaba da halayyar marigayin da kuma zuriya ta gari da ya fito, ta Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, yana mai cewa bayan barinsa aikin gwamnati, ya ci gaba da kasancewa jigo mai kula da ɗabi’u da al’adun Daular Sakkwato da kuma kare martabarsu.

    Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, rasuwar Alhaji Abubakar Alhaji babban rashi ne ba kawai ga iyalansa da al’ummar Jihar Sakkwato ba, har ma ga Arewa da daukacin Najeriya, waɗanda suka amfana sosai daga ɗimbin gogewa, jagoranci na gari, da kuma shawarwarinsa masu fa’ida ga ƙasa.

    A madadin Gwamnonin Jihohin Arewa 19, Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, Sarkin Musulmi, Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da ƙasar Sakkwato, da Gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato, da kuma dokacin ‘yan Najeriya dake cikin jimamin rashin wannan babban dattijo.

    Ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta wa marigayi Alhaji Abubakar Alhaji kurakuransa, ya kuma saka masa da Aljanna Firdausi saboda gudummawar da ya bayar ga al’umma.

     

    alh arewa gwabnonin taaziyya
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleThe North and The Politics of Consumption
    Next Article Shugaba Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Ministan Kuɗi, Alhaji Abubakar Alhaji

    Related Posts

    News

    ZAMFARA FARMERS CRY OUT AS QUEALA BIRDS RAVAGES FARMS IN BAKALORI IRRIGATION AREAS.

    July 31, 2026
    News

    RECONSTRUCTION OF MANDO -BIRNIN GWARI ROAD TO COMMENCES SOON.

    July 31, 2026
    News

    Shugaba Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Ministan Kuɗi, Alhaji Abubakar Alhaji

    July 31, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026275 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026235 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026213 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026159 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026156 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.