Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhini kan rasuwar tsohon Ministan Kuɗi kuma fitaccen ɗan siyasa, kuma jami’in gwamnati, Alhaji Abubakar Alhaji, wanda ya rasu yana da shekaru 85.
A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu hidimar ƙasa, wanda ya shafe shekaru da dama yana aiki a manyan muƙaman gwamnati.
Shugaban ya ce marigayi Sardaunan Sakkwato ya yi fice a fannin gudanar da mulki, tare da nuna ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin kuɗi da kuma diflomasiyya, lamarin da ya ba da gagarumar gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da siyasar Najeriya.
Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, Majalisar Masarautar Sakkwato da daukacin iyalan gidan sarautar bisa wannan babban rashi.
Haka kuma, ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Sakkwato, al’ummar jihar, da abokan hulɗa da ɗaliban da marigayin ya koyar tare da jagoranta a sassa daban-daban na ƙasar.
Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa Alhaji Abubakar Alhaji, Ya saka masa da Aljannatul Firdausi saboda hidimomin da ya yi wa ƙasa da al’umma, sannan Ya bai wa iyalansa da al’ummar Sakkwato haƙurin jure wannan babban rashi.

