Daga Aliyu Samba
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce iƙirarin dawo da tallafin man fetur da wasu ‘yan siyasa ke yi nuni ne da “jahilci mai tsanani kan shugabanci da tattalin arziki.”
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Shugaban ya ce kafin zuwansa kan mulki, jihohi 27 ba sa iya biyan albashin ma’aikatansu, balle kuma fansho, yana mai cewa albashin ma’aikata na ciyar da iyalai tare da taimaka wa tattalin arzikin jihohi.
Ya ce cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnati damar ƙara kuɗaɗen da take amfani da su wajen gina hanyoyi, gidaje, makarantu da asibitoci, tare da farfaɗo da harkokin kiwon lafiya da horar da malamai da ma’aikatan lafiya.
Tinubu ya kuma taya Adeleke murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan Osun, yana mai cewa al’ummar jihar sun zaɓe shi domin ya ci gaba da jagorantar su.
Ya buƙaci ‘yan siyasa su mutunta sakamakon zaɓe tare da gina haɗin kai, yana mai cewa, “ba galaba ka yi a kan kowa ba, ka ci zaɓe ne. Wannan shi ne ainihin dimokuraɗiyya.”
Sabuwar Nigeria.

