Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » *Rasuwar Sarkin Gumel Babban Rashi ce ga Masarautun Gargajiya da Nijeriya* – Kashim Shettima
    News

    *Rasuwar Sarkin Gumel Babban Rashi ce ga Masarautun Gargajiya da Nijeriya* – Kashim Shettima

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 4, 20262 Mins Read
    IMG 20260902 WA0013
    IMG 20260902 WA0013

    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Mai Martaba Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, CON, a matsayin babban rashi ga Jihar Jigawa da Nijeriya baki ɗaya.

    Shettima ya ce marigayi Sarkin ya kasance daga cikin sarakunan gargajiya da suka sadaukar da shekaru masu yawa wajen tabbatar da zaman lafiya, bunƙasa ilimi, ci gaban al’umma da ƙarfafa haɗin kan ƴan ƙasa.

    Mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Jihar Jigawa, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin da Masarautar Gumel, inda ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya.

    Marigayi Sarkin Gumel na 16 ya rasu a birnin Alkahira na ƙasar Masar a ranar 3 ga Satumba, 2026, bayan shafe kusan shekaru 46 yana mulkin masarautar. Ya hau karagar mulki ne a ranar 16 ga Disamba, 1980.

    Mataimakin Shugaban Ƙasan ya ce za a tuna da marigayi Sarkin ne saboda tsawon mulkinsa, tare da hikima, zaman lafiya da kishin al’ummar da ya nuna wajen gudanar da shugabancinsa.

    Ya bayyana shi a matsayin uba, mai haɗa kan jama’a, kuma mai bayar da shawarwari, wanda hikimarsa ta taimaka wajen hidimtawa al’umma da ƙasa tsawon kusan rabin ƙarni.

    Shettima ya ce duk da cewa mulkin marigayin ya gudana a lokacin da Nijeriya ta fuskanci sauye-sauyen siyasa da zamantakewa da dama, ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, ilimi, karatun addinin Musulunci da zaman tare cikin lumana.

    Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana matuƙar girmama marigayi Sarkin, musamman bisa gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

    Shettima ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi, tare da ba iyalansa, Masarautar Gumel da al’ummar Jihar Jigawa haƙurin jure wannan babban rashi.

    emir gumel mourn Shettima vp
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Radda Receives PAN MD, FCMB Pensions Executive
    Next Article TROOPS OF OPERATION FANSAN YAMMA RESCUE THREE KIDNAPPED VICTIMS IN KATSINA STATE

    Related Posts

    News

    Governor Radda Receives PAN MD, FCMB Pensions Executive

    September 4, 2026
    News

    PHOTO CAPTION RADDA ATTENDS WEDDING FATIHA IN KANO

    September 4, 2026
    News

    COMMUNITIES IN IKARA ,ANCHAU, KADUNA STATE HAILS UBA SANI RURAL TRANSFORMATION PROJECTS.

    September 4, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026294 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026242 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026226 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026168 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026165 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026156 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.