Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Zurmi
    News

    Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Zurmi

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 2, 20262 Mins Read
    FB IMG 1788367526664
    FB IMG 1788367526664

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Mai Martaba Alhaji Bello Sulaiman, wanda ya rasu a ranar Litinin, bayan shafe shekaru biyar a kan karagar mulkin masarautar.

    A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zurmi, Gwamnatin Jihar Zamfara da al’ummar jihar, da kuma daukacin masarautun Najeriya.

    Read also: JAGA’S ROUTINE: ENGR JAMIL JAGA JOINS KADUNA POLITICAL LEADERS IN GROUNDBREAKING AND COMMISSIONING MAJOR DEVELOPMENT PROJECTS ACROSS ZARIA AND SOBA LGA.

    Read also: GOBARA TA ƘONE ƊAKUNAN KWANAN ƊALIBAI UKU A MAKARANTAR MAHIYYA GLOBAL ACADEMY DA KE KAURA NAMODA

    Shugaban ya bayyana marigayin a matsayin basaraken da ake girmamawa, wanda ya jagoranci al’ummarsa cikin hikima, mutunci da jajircewa a wani lokaci mai matuƙar wahala. Ya ce marigayin ya nuna ƙwarewar jagoranci wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi masarautar Zurmi.

    Read also: I’ve Paid Over N7bn As Compensation To Property Owners—Uba Sani

    Tinubu ya ce Sarkin ya kasance jigo wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da juriya a tsakanin al’ummarsa, yana mai cewa shawarwarinsa masu hikima da ƙoƙarinsa na samar da zaman lafiya sun taimaka ba kawai ga Masarautar Zurmi ba, har ma da Jihar Zamfara da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Yamma.

    Shugaban Ƙasar ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya saka masa da alheri kan ayyukan da ya yi, Ya kuma ba shi Aljannar Firdausi. Ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalansa da duk waɗanda rasuwar ta shafa haƙuri da ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

    emir mourns pbat zurmi
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGOVERNOR FUBARA REAFFIRMS COMMITMENT TO NIGERIAN ARMY AND SECURITY AGENCIES IN RIVERS STATE
    Next Article TROOPS OF OPERATION FANSAN YAMMA NEUTRALISE TERRORISTS, INTERCEPT AMMUNITION COURIER IN ZAMFARA AND KADUNA STATES

    Related Posts

    News

    GROUP PRAYS FOR SPEEDY RECOVERY OF ABDULSALAMI, SEN. MUSA

    October 18, 2026
    News

    GOBARA TA ƘONE ƊAKUNAN KWANAN ƊALIBAI UKU A MAKARANTAR MAHIYYA GLOBAL ACADEMY DA KE KAURA NAMODA

    October 18, 2026
    News

    JAGA’S ROUTINE: ENGR JAMIL JAGA JOINS KADUNA POLITICAL LEADERS IN GROUNDBREAKING AND COMMISSIONING MAJOR DEVELOPMENT PROJECTS ACROSS ZARIA AND SOBA LGA.

    October 18, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Retired Police Officers Give FG, PENCOM, IGP October 15 Deadline Over Pension Demands

    October 12, 2026373 Views

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026343 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026260 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026250 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026194 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026177 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.