Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yi masa fatan ƙarin shekaru masu albarka cikin ƙoshin lafiya da nasara.
A cikin saƙon taya murnar, Shugaba Tinubu ya bayyana Badaru a matsayin gogaggen mai gudanarwa, ɗan kasuwa mai nasara kuma jajirtaccen ɗan siyasa wanda ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa. Ya tuna da irin ayyukan da tsohon gwamnan ya aiwatar a fannonin noma, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa zamantakewa a lokacin da yake jagorantar Jihar Jigawa daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Shugaban ya kuma yaba da irin hidimar da Badaru ya yi wa ƙasa a matsayin Ministan Tsaro daga watan Agustan 2023 zuwa Disamban 2025, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai kyakkyawar mu’amala da kishin ƙasa. Ya ce Badaru, wanda aka fi sani da Sardaunan Ringim, ya yi amfani da nasarar da ya samu a harkokin kasuwanci, musamman ta hannun kamfaninsa na Talamiz Group, wajen bayar da gudunmawa a hidimar jama’a.
Haka kuma, Tinubu ya yaba da biyayya da goyon bayan Badaru ga jam’iyyar APC, musamman rawar da yake takawa a matsayin Darakta-Janar na ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A). Shugaban ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa tsohon gwamnan lafiya, ƙarfi da tsawon rai, tare da ba shi ikon ci gaba da yi wa Najeriya hidima.

