Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Sakatare-Janar na Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed, wanda ya rasu da sanyin safiyar Talata bayan tsawon shekaru yana hidimtawa addinin Musulunci da ƙasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tasiri, wanda ya jagoranci harkokin Majalisar Koli ta Shari’a cikin hikima, hangen nesa da kishin haɗin kan al’umma, adalci da zaman lafiya.
Read also: NAF JET CRASH: Governor Radda Condoles President Tinubu, Ondo Govt and Victims Families
Shugaban ya tuna da doguwar alaƙar da ke tsakaninsa da marigayin, musamman tun daga shirye-shiryen zaɓen shekarar 2011, da kuma shekarun baya, inda Malam Baba-Ahmed ya kasance cikin waɗanda suka ba shi shawarwari tare da mara masa baya a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Read also: PRESIDENT TINUBU MOURNS NAF PERSONNEL IN ONDO JET CRASH, ORDERS THOROUGH INVESTIGATION OF THE MISHAP
A cewar Shugaba Tinubu, marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Majalisar ta ci gaba da bayar da gudummawarta kan muhimman batutuwan ƙasa, tare da ƙarfafa fahimtar juna da kuma yaɗa kyawawan ɗabi’u, adalci da gyaran zamantakewar al’umma.
Shugaban Ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya, shugabanni da mambobinta, iyalan Baba-Ahmed, gwamnatin da al’ummar Jihar Kaduna, da kuma daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya bisa wannan babban rashi.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya jikansa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.

