Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Yadda ’Yan Najeriya Za Su Nemi Lamunin Gwamnati Don Ginawa Ko Siyan Gida
    News

    Yadda ’Yan Najeriya Za Su Nemi Lamunin Gwamnati Don Ginawa Ko Siyan Gida

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 18, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787056624631
    FB IMG 1787056624631

    ’Yan Najeriya na iya samun damar karbar lamunin gidaje daga Bankin Lamuni na Gidaje na Tarayya (FMBN) ta hanyar Asusun Gidaje na Kasa (NHF), domin sayen gida, gina sabon gida ko gyara wanda suke da shi.

    A halin yanzu, shirin NHF Mortgage Loan na bai wa masu bayar da gudummawar NHF damar samun lamuni har zuwa Naira miliyan 50, gwargwadon karfin biyan bashin da kuma darajar gidan. Ana karbar lamunin ne da riba da ba ta wuce kashi shida cikin 100 a shekara, yayin da mafi tsawon lokacin biyan bashin ya kai shekaru 30.

    Read also: PRESIDENT NAOWA EXTENDS HOPE, SUPPORT TO TEACHERS, WIDOWS OF FALLEN HEROES AND MILITARY SPOUSES IN KADUNA

    Domin samun lamunin, dole ne mutum ya kasance dan Najeriya mai shekaru 18 ko sama da haka, ya kasance mai bayar da gudummawa ga NHF na akalla watanni shida a jere, sannan ya kasance yana da tabbataccen hanyar samun kudin shiga. Haka kuma, dole ne a nemi lamunin ta hannun bankin jinginar gidaje na farko (Primary Mortgage Bank) ko wata cibiyar bada lamuni da FMBN ta amince da ita.

    Read also: MINISTER OF LIVESTOCK DEVELOPMENT APPLAUDS AGRICULTURAL DRIVE OF GOVERNOR UMARU BAGO

    Mai neman lamunin zai fara tabbatar da matsayin asusun NHF dinsa, sannan ya zabi wata cibiyar jinginar gidaje da FMBN ta amince da ita domin samun fom da sauran bayanan da ake bukata. Daga cikin takardun da ake iya bukata akwai shaidar gudummawar NHF, bayanan albashi ko kudin shiga, takardun mallakar fili ko gida, rahoton tantance darajar kadarar da kuma adadin kudin da ake bukata dan sayen ababen gini (Bill of Quantities) idan ana neman kudin gina gida.

    Read also: Governor Inuwa Yahaya Arrives Maiduguri for North-East Governors’ Forum Meeting

    Bayan an gabatar da takardu, bankin jinginar gidajen zai tantance karfin mai nema na biyan bashin da kuma sahihancin takardun kadarar. Daga nan za a gudanar da binciken shari’a da tantance darajar gidan kafin amincewa da lamunin da kuma fitar da kudin domin manufar da aka amince da ita. Masu neman lamuni kuma su yi hattara da masu damfara da ke ikirarin za su taimaka musu su samu lamuni ta hanyar karbar kudi, domin FMBN na gargadin jama’a da su yi hulda da hukumomin da aka amince da su kawai.

    Don fara nema ko duba bayanan shirin, za a iya ziyartar shafin hukuma na FMBN: https://fmbn.gov.ng/products/nhf_mortgage_loan

    gidaje gina lamunin
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleDEFENCE MINISTER VISITS NIGERIAN AMBASSADOR TO THE UNITED STATES OF AMERICA IN WASHINGTON D.C.
    Next Article CHAIRMAN ZARIA LOCAL GOVERNMENT ENGR JAMIL JAGA HANDS OVER NEWLY PROCURE ARMOURED PERSONNEL CARRIER TO COMMANDANT MOPOL 47.

    Related Posts

    News

    PRESIDENT NAOWA EXTENDS HOPE, SUPPORT TO TEACHERS, WIDOWS OF FALLEN HEROES AND MILITARY SPOUSES IN KADUNA

    October 3, 2026
    News

    Governor Inuwa Yahaya Joins North-East Colleagues at State Banquet Ahead of 13th NEGF Meeting in Maiduguri

    October 3, 2026
    News

    VP Shettima to Launch Nigeria for Women Programme in Katsina

    October 2, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026316 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026252 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026239 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026178 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026174 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026164 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.