Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Asusun Tallafawa Daliban manyan makarantu,NELFUND ya Yabawa Shugaba Tinubu Kan Dorewar Tallafin Lamunin Dalibai
    News

    Asusun Tallafawa Daliban manyan makarantu,NELFUND ya Yabawa Shugaba Tinubu Kan Dorewar Tallafin Lamunin Dalibai

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 24, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787602695703
    FB IMG 1787602695703

    Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kudurin tabbatar da dorewar tsarin ba da lamunin karatu ga daliban Najeriya.

    NELFUND ta ce Shugaban Kasar ya umurci a karkatar da kudaden da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran laifukan Tattalin Arziki (EFCC) ta kwato, zuwa asusun NELFUND domin karfafa tallafin lamunin karatu.

    A cikin wata sanarwa da Daraktar Sadarwa ta NELFUND, Mrs Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar ranar 19 ga Agusta, 2026, asusun ya kuma yi maraba da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) kan tura ribar da ba a karba ba daga Capital Market Trust Fund da Dormant Account Trust Fund zuwa NELFUND.

    NELFUND ta ce matakan za su taimaka wajen samar da ingantaccen tushe na kudaden da za su ci gaba da tallafa wa shirin lamunin dalibai yayin da yawan masu neman tallafin ke karuwa.

    A cewar asusun, zuwa watan Agustan 2026, NELFUND ta riga ta fitar da sama da Naira biliyan 322 ga dalibai, daga cikin masu neman lamunin karatu sama da miliyan 1.6 da aka gabatar.

    Shugaban Hukumar Gudanarwar NELFUND, Jim Ovia, ya bayyana godiya ga Shugaba Tinubu bisa ci gaba da goyon baya da amincewar da yake bai wa asusun, yana mai cewa hakan ya kara karfin kudurin gwamnatin na tabbatar da cewa rashin kudi bai zama dalilin hana wani dan Najeriya samun ilimi mai zurfi ba.

    Shi ma Manajan Daraktan NELFUND, Akintunde Sawyer, ya ce sabon kudurin Shugaban Kasa ya nuna irin muhimmancin da gwamnatin ke bai wa ilimi, tare da kokarin gina tsarin ba da lamunin karatu mai dorewa.

    Sawyer ya tabbatar da cewa NELFUND za ta ci gaba da amfani da dukkanin kudaden da aka damka mata cikin gaskiya da rikon amana, domin amfanin daliban Najeriya.

    NELFUND ta ce sabon tsarin samar da kudade zai kara wa Gwamnatin Tarayya karfin fadada shirin da kuma kai lamunin karatu ga karin daliban Najeriya da suka cancanta.

    FB IMG 1787602745123
    FB IMG 1787602745123
    education nelfund sustainance
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleDawo da tallafin man fetur zai mayar da Najeriya baya — Mohammed Idris
    Next Article Shugaba Tinubu ya taya Mai Alfarma Sarkin Musulmi murnar cika shekara 70

    Related Posts

    News

    OPERATION HADIN KAI STRENGTHENS PARTNERSHIP WITH UNIVERSITIES FOR ENHANCED CAMPUS SECURITY

    August 25, 2026
    News

    EID-EL-MAULUD: FARMER GOVERNOR UMARU BAGO CALLS FOR RENEWED PRAYERS FOR THE NATION.

    August 25, 2026
    News

    Governor Radda Greets Sultan of Sokoto at 70, Says He’s a Bridge Builder

    August 24, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026289 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026241 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026223 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026165 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026159 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.