Sabuwar Nigeria.
Aci gaba da dubiyan manyan ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa,karkashin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ a Arewacin Najeriya, Ayarin zakakuran manema labarai dake rangadi tare da Babban Mai taimakawa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, sun kai ziyara zuwa sashe na farko na aikin hanyar Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato, wato ɓangaren Zariya–Funtuwa–Sheme, domin duba yadda aikin ke gudana da kuma tantance ci gaban da aka samu.
A yayin ziyarar, an bayyana wa ayarin cewa aikin hanyar na daga cikin manyan ayyukan more rayuwa da gwamnatin tarayya ke bai wa fifiko saboda muhimmancinsa ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Duk da cewa an amince da aikin tun a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙara masa ƙarfi ta hanyar amincewa da mayar da shi daga hanya mai layi ɗaya zuwa babbar hanya mai tagwaye biyu (Dual Carriageway), domin dacewa da yawan zirga-zirga da kuma biyan buƙatun ci gaban yankin.
Jami’an Kula da aikin sun bayyana cewa hanyar za ta haɗa jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara da Sakkwato, tare da sauƙaƙa zirga-zirgar matafiya, jigilar kayan amfanin gona, dabbobi da sauran kayayyakin kasuwanci.
Sun ƙara da cewa aikin ya haɗa da sake gina hanyar gaba ɗaya, ƙarin layukan mota, gadoji, magudanan ruwa da sauran kayan tsaro na zamani domin rage haɗurra, sauƙaƙa tafiya da kuma inganta rayuwar masu amfani da hanyar.
Baya ga inganta sufuri, aikin ya riga ya samar da dubban guraben ayyukan yi ga injiniyoyi, masu sana’o’in hannu, ma’aikatan sarrafa injuna da sauran ma’aikata a wuraren da ake gudanar da aikin.
Ana kuma sa ran da zarar an kammala shi, zai ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci, da jawo masu zuba jari, da rage kuɗin sufuri da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihohin Arewa maso Yamma da sauran sassan Najeriya.
Masu aikin jaridar da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ sun bayyana cewa rangadin ya ba su damar gani da ido kan irin sauye-sauyen da ake samu a fannin ababen more rayuwa.
Sun bayyana cewa aikin hanyar da ta tashi daga Zariya–Funtuwa–Sheme wata muhimmiyar shaida ce ta ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta hanyar gina ingantattun hanyoyi da za su bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummar Najeriya.





