Sabuwar Nigeria.
Wannan aikin dai muhimmi ne da zai inganta samar da lantarki da kakkafa masana’antu da Kuma bunkasa tattalin arzikin Arewacin Kasar nan
A rana ta uku na rangadin ‘Gani Ya Kori Ji’ na manyan ayyukan gwamnatin tarayya a Arewacin Najeriya, Ayarin masu aikin yada labarai da ke rangadi tare da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, Sun kai ziyara zuwa aikin Shinfida bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), ɗaya daga cikin manyan ayyukan samar da makamashi da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa.
Wannan ga ni da Ido, ya bai wa wakilan Ayarin damar ganin yadda aikin ke gudana da kuma samun cikakken bayani daga jami’an da ke kula da aikin.
A yayin ziyarar, Ayarin sun fara isa Block Valve Station 19 da ke ƙauyen Rahma Wali a Ƙaramar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna, inda jami’an aikin suka bayyana cewa aikin ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na kammaluwa.
Sun nuna kwarin gwiwar cewa da zarar an ƙaddamar da aikin, zai samar da iskar gas mai ɗorewa ga tashoshin samar da wutar lantarki da masana’antu, lamarin da zai rage kuɗin makamashi, ƙara samar da lantarki da kuma buɗe ƙofofin kafa sabbin masana’antu a Arewacin ƙasar.
Jami’an sun bayyana cewa aikin, wanda aka fara a zamanin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, na ci gaba da samun cikakken goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda).
Sun ce wannan ya nuna ƙudirin gwamnatin tarayya na kammala manyan ayyukan more rayuwa da ke da tasiri kai tsaye ga bunƙasar tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
An kuma yi wa Ayarin bayanin cewa bututun iskar gas na AKK mai tsawon kusan kilomita 614 zai haɗa yankunan da ake da wadataccen iskar gas a kudancin Najeriya da jihohin Arewa, tare da samar da ingantaccen makamashi ga masana’antu, kamfanonin sarrafa kayayyaki da sauran harkokin kasuwanci.
Baya ga haka, aikin ya samar da dubban guraben ayyukan yi kai tsaye da kuma a fakaice a lokacin gini, kuma ana sa ran zai ƙara samar da ɗimbin ayyukan yi bayan fara aiki sakamakon sababbin masana’antu da harkokin kasuwancin da za su bunƙasa a yankunan da bututun ya ratsa.
Masu aikin jaridar da ke cikin shirin ‘Gani Ya Kori Ji’ sun bayyana cewa ziyartar aikin ta ƙara musu fahimtar muhimmancin shirin ga makomar tattalin arzikin Arewa.
Sun ce aikin ba kawai bututun iskar gas ba ne, amma wata babbar gada ce ta bunƙasa masana’antu, ƙarfafa samar da makamashi, jawo masu zuba jari da samar da ci gaba mai ɗorewa.
Sun kuma bayyana aikin a matsayin wata babbar shaida ta ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da manyan ayyukan more rayuwa wajen inganta rayuwar al’umma da dora tattalin arzikin Najeriya a Kan tafarki mai dorewa.







