Kotun daukaka Kara da ke zamanta a Abuja,ta janye hukuncin da wata kotu ta yanke da ta umurci hukumar zabe ta kasa ta soke rajistan Janiyyar ADC,da wasu jamiyyun hudu,da ake zargin sun kasa cimma kaidojin rajista da tsarin mulki ya tanaza.
A Wani hukuncin bai daya da Alkalan kotun su you suka zartar,sun amince cewar umrnin da Babbar kotun ta baiwa hukumar Zaben a ranar 15 ga watan nan batacce ne.
Kotun ta ce Babbar kotun ta yi kuskuren saurararon karar tun da ba ta da hurumi,sannan ta yanke hukuncin a karar da Sam ba ta da hurumin saurara da Wani ya shigar.
Kamar yadda kotun ta ce,babu halataccen karar da aka shigar da zai sa babbar kotun gangancin yanke hukuncin da ya umurci hukumar zabe ta soke rajistan jamiyyun.
Ta kura cewar babbar kotun da ta saurari karar ta kasa tantance dukkan hujoji da shedun da aka gabatar ma ta,tana mai cewa kotun ta kekasa kasa ta Yi biris DA hujjar da aka gabatar ma ta ,cewa jamiyyun sun lashe kujeru da dama a zabubbukan DA suka gabata.
Har Ila yau kuma kotun ta lura cewa babbar kotun ta Ki yarda ta yi aiki da umrnin da aka ba ta,cewer ta dakatar da sauraron shariar.
Ta kara da cewa da ya kamata a ce babbar kotun ta yi watsi da wannan karar saboda rashin hurumi da cancanta.
Saboda haka kotun daukaka karar,a hukuncin da Mai sharia Abba Muhammed ya karanta,sun yarda cewar rajistan jamiyyun suna nan daram.
Sun kuma amince da daukaka daban daban da jamiyyun siyasar suka shigar,da Kuma neman wadanda suka shigar da karar,wato Kungiyar tsoffin Yan majalisa ta kasa su biya wasu kudade ga wadanda aka kai karar.
Rahotani sun ce baya ga Janiyyar ADC, sauran jamiyyun da abin ya shafa sun hadar da jamiyyun da kotun daukaka karar ta dawo da rajistan su,sun hadar da jamiyyun APP, AA,da AP,da Kuma ZLP.
Idan dai Za a iya tinawa, kotun daukaka karar a ranar 16 ga watan yuni ta ba da umrnin dakatar da aiki da wannan hukuncin na babbar kotun tarayya,ta kuma kakkauaar sikar alkalin babbar kotun da ya saurari shariar, saboda yadda ya ki aiki da umrnin kotun daukaka karar.
Alkalan kotun daukaka karar sun caccaki mai Sharia Peter Lifu na babban kotun tarayya Abuja,saboda ya kekasa kasa ya ki bin umrnin kotun daukaka karar ta bayar a ranar 22 ga watan mayu inda ta umurce shi da ya dakatar da sauraron karar,har sai sun kammala sauraron daukaka karar da jamiyyun suka shigar.
Sun lura cewa kodayake an janyo hankalin alkalin babbar kotun Akan umurnin da ta bayar na dakatar da sauraron karar,amma ya yi biris da umurnin,har ma ya yi gaban kansa ya yanke hukuncin.
Kotun daukaka karar ta ce abin da mai Sharia Lifu ya yi sam bai dace ba,tana mai cewa kotun koli a wani hukuncin da ta yanke a baya,ta ce duk alkalin da ya yi irin wannan danyen aikin,sam bai cancanci zama alkali ba, saboda abin da ya aikata bai dace ba.
Babbar kotun dai ta umurci hukumar zabe ta kasa ta soke rajistan jamiyyun su biyar, wadanda ta ce sun kasa cika shariddan kundin tsarin mulkin kasa da ake bukata don ci gaba da wanzuwarau da shiga a dama da su a zabubbukan da ke tafe.
Haka nab Kuma babbar kotun ta harantawa hukumar zabe ta kasa daga ci gaba da amincewa da jamiyyun, da kin amincewa da dukkan yan takarar su, Ko muamala da su don shiga zaben 2027.
Mai sharia Lifu ya Kuma umurci wadanda aka kai karar su daina ayyana kansu a matsayin jamiyyun da Ke da rajista a Kasar nan,yana mai cewa akwai hujja a karar da masu suka shigar
Masu karar dai sun dage cewar ci gaba da wanzuwar Janiyyar ADC da sauran jamiyyun da aka kai karar a matsayin jamiyyun da ke da rajista,ya sabawa doka,kuma zai sa alamun shakku a tsarin zabe a kasar nan.
Sai dai kuma wani abin da ya bayyana Shi ne cewar Shi kansa Antoni janar Na tarayya kuma ministan sharia Lateef Fagbemi SAN wanda shi ma ya Ke cikin wadanda aka kai karar ya goyi bayan wadanda ake karar.

