Prof. Sulaiman Abdullahi Karwai
Ko shakka babu, gwamnonin jihohi sun sami gagarumin ƙarin maƙudan kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya sakamakon tsauraran matakan tattalin arziki da gwamnatin ta dauka, musamman cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a hada-hadar canjin kuɗi.
Duk da wannan ƙarin kuɗi mai yawan gaske, masana kimiyyar tattalin arziki da zamantakewa suna ta ƙorafi akan cewa wasu gwamnonin Arewa ba sa yin amfani da waɗannan maƙudan kuɗaɗen wajen fifita lamuran taɓarɓarewan tsaro da suka gagari Kundila, da rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da sama wa matasa ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai da shawo kan ƙazancewar harkar kiwon lafiya da ilimi a jihohinsu.
Shi ma shugaban gwamnatin tarayya ya kasa kai bantansa. Duk da ambaliyan kuɗaɗen shiga da gwamnatin take samu, shugaban ƙasa ya sa bashi ya yi wa Najeriya ɗaurin gwarmai. Saboda rahoton Ofishin Kula da Bashin Ƙasa (DMO) ya nuna cewa jimillar bashin al’ummar ƙasa ya kai Naira tiriliyon 159.28 (31/12/2025). Wannan na nufin shugaban ƙasa ya ƙaƙabawa kowane ɗan Najeriya bashin kimanin N657,000.00 (in anyi amfani da mutum miliyan 242.4). Cibiri Nannagi, wani kaya sai amale!
Bayan wani balaguro da yasa na karaɗe kasar nan, na yi wani dogon rubutu a ranar 22/6/2025 da na sa masa taken: “GA WANI ABU A KAN MATAR SARKI”; na yi tsokaci game da yadda na ga yadda rashin aiki da kamfanoni da masana’antu da mayatar talauci da jahilci da yunwa suka addabi biranen mu da ƙauyuka. Amma gwamnatocin jihohin kudancin Najeriya, sun haɗa ƙarfi da ƙarfe suna gwangwaje al’ummar su da kamfanoni da masana’antu da ilimin zamani da sama wa matasa ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai da jajircewa wajen samar da mafita ta dindindin ga rashin tsaro. Alal misali, muna cikin tafiya a mota tsakanin Ilori da Osogbo sai kaga mace da ƴaƴanta ƙanƙana sun sauka wajen ƙarfe 12:30 na dare sun kama hanyar daji zuwa kauyen su.
Ƴan kwanaki da suka shuɗe, wani aiki ya sa na je wasu jihohin Yamma maso Arewa da Gabas maso Arewa da tsakiyar Najeriya. Tabbas, gwamnonin mu sun bar jaki suna bugun taiki.
Bana cikin waɗanda suke ganin cewa gwamnonin Arewa suna siyawa sarakuna motocin alfarma a matsayin wani yunkurin basu cin hanci ko yin almubazzaranci da dukiyar al’umma. Na yi shakulatin bangaro da ilimina na “Leadership and Human Resource Management” da na “Leadership and Management of Change” don na gabatar da ‘uzurin’ gwamnonin mu da suka ba da himma sosai wajen kashe maƙudan kuɗaɗe a wajen sharholiya da baɗala wajen bikin iyalansu da ba ƴaƴansu maƙudan dukiyar jama’a da aka basu amana domin ƴaƴansu su hole a ƙasashen waje da suna neman ingatattan ilimi; da ɓangaren gina tashoshin jiragen sama da gadojin sama da musu kwalliya.
Amma halin ko in kula da wasu gwamnonin mu ke mana a bangaren ilimi da kiwon lafiya, da talauci da yunwa da gungun almajirai da zauna gari banza da ɓata-gari da annobar hijirar matasa zuwa kudancin Nijeriya; da rashin tashi haiƙan wajen samar wa matasa Ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai (abinda ya taimaka matuƙa da gaske wajen ƙyanƙyashe mayaƙan Boko Haram da ‘yan ta’addada da bandits (‘yan bindigan daji) da ‘yan kidnafin); da _ƙusuri_ wajen lalubo bakin zaren warware wadannan matsalolin, ya sa na lashe aman da na yi.
A wannan lokacin, na ga bala’o’in da wasu gwamnoni suka jefa al’ummarsu a ciki. Kama daga rashin ruwan sha da rashin malamai da ingantattun makarantu da asibitoci isassu na zamani har zuwa yaɗuwan talauci da ƴan ƙwaya da kuma ƴan shaye-shaye.
Alal misali, wani Gwamnan jihar da take fama da wasu daga bala’o’in da aka ambata, ya yi matuƙar ƙoƙari wajen gwangwaje sarakunan jihar da motocin alfarma sama da 150, kuma yana ta gina gadojin sama a ‘ko ina’ a babban birnin jihar. Bugu da ƙari, akwai jihar da ake labarta cewa ta fi kowacce jiha a Najeriya fatara da matsalolin tsaro da bandits da ‘yan kidnafin da ‘yan ta’addada, amma wani gwamnan ta ya dinga gwangwaje sarakunan jihar, da wasu da baza a iya ambaton su ba, da motocin alfarma. Amma ga ƴan gudun hijira da mata da aka kashe mazansu da marayu suna halin ƙaƙanikayi.
Akwai jihar da ba wani abun ci-gaba da za ka gani a babban birninta da yafi gadojin sama. Hasalima, AliCASH yayi wani katafaren wajen koyan sana’o’in dogaro da kai, amma tunda ƴaƴan talakawa ne za su ci muriyar wajen, sai akace gwamnatin jihar ta garƙame wajen.Tambayi Dan Bello ka sha labari. Haka zalika, “Baba mai Tazarce” (Allāh SWT ya jiƙansa da rahama) ya gina babbar ma’aikatar harkokin koyan sana’o’in dogaro da kai, amma wajen yana nan “la _ya mutu wala Yahye_ “. Da, lokacin da ake da gwamnoni masu kishin ƙasa, musamman Ɗan Sandan cikinsu, wannan jihar ita ta fi kowacce jiha a Arewa a bangaren ilimi da noma da kiwon lafiya da kasuwanci. Allāh SWT ya jiƙan “Baƙon” da ya assasa tubalin raya wannan jiha.
Akwai zargi mai tushe da yake nuna cewa mafi yawan kwangiloli masu tsoƙa ‘jarfata’ ce da ‘yan Kudu su ke da ‘hauzi’ a wasu jihohin. Wai su suka ƙware wajen rufe asirin “His Excellency” da ‘fulogansa’.
Gwamnonin mu suna ganin inda Musulmi suka zama saniyar ware a wasu jihohin Kudancin Najeriya – inda ake kashesu ake lalata dukiyarsu. Ko inda samarin mu da sukayi gudun hijira, saboda an ƙone garuruwansu kokuma sun zama kufai ko harcen fatara ya kusa lanƙwamesu, suke yin aikin ƙasƙanci ko aikin masha’a. Abin ma ya kai ga in wasu Musulmai sun zo wucewa ta wata jiha a nan Arewa, sai a musu kisan gilla ko kisa kiyashi.
Kaga lamarin kisan kiyashin da aka yi wa Musulmi da suke dawowa daga Mauludi daga jihar Bauchi da “Hausawan” Zariya 13 da suka tafi daurin aure da babbar motar Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, da Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya) da sauran kashe-kashen baya-bayan nan a jihar yaƙi ci, ya ƙi cinyewaya. A cikin shekaru sama da 25 da suka shuɗe, an tursasawa Musulmi yin hijira daga jihar zuwa wasu jihohin saboda jihar ta zama dandalin “kare-jini-biri-jini”. Gwamnonin mu suna ganin wannan zaluncin ƙarara amma sun kasa samo mana mafita.
Ina mutuƙar mamaki, ace gwamnonin mu har yanzu basu gane da alaƙar wannan jihar ba da Isra’ila. Akwai ɗan Majalisar wakilai ta tarayya da yayi iƙirarin cewa wannan jihar ta aika mutane 200 zuwa Isra’ila domin su koyi atisaye. Daɗi da ƙari, a rikicin baya-bayan nan an sami ɗan Amurka, haka kuma an taɓa samun wani da kayayyakin yaƙi amma wai sai aka tisa ƙeyarsu zuwa garinsu. Kuma, yanzu ya fito fili ƙarara daga baƙin ƴan Majalisar Amurka da masu fada a ji cewa gwamnatin Amurka da silar CIA su suke kafa ƙungiyoyin ta’adda a duniya kāfataninta da taimakawa da makudan kuɗaɗe.
Muna fargaba, kar gwamnonin mu su zama kamar shugabannin larabawa na Gabas ta Tsakiya. A farkon lamari, sun ɗauka ƙasar Isra’ila ba za ta yi wani tasiri ba. Saboda haka suka shagala da shan shayi da cin shika-kaza suna kiran ƙisar Isra’ila (دولة مزعومة); suka dauki tsaron kasashensu suka ba uwargidan Isra’ila. Yanzu da gari ya waye, sai suka zamo su ne (دول مزعومة). Bahaushe dai ya ce: ina gemun ɗan’uwanka ya kama wuta… Allāh SWT ya jiƙan Sardauna, Gamji Uban ‘yan boko.
Ya kamata gwamnonin mu na Arewa su gane cewa mu abin da muke rokon su shine su zamo shugabanni na gari masu adalci da riƙon amana. Mu al’umma da muƙe zaɓen su bai cancanta su sa mu cikin bala’o’i da matsaloli ba; su bar mu da ƴan ƙwaya da mashaya, su kuma da iyalansu da ‘fulogansu’ su dinga wadaƙa da almubazzaranci da dukiyar jama’a da aka basu amana.
Ina tsoron kar abinda Cif Obafemi Jeremiah Oyeniyi Awolowo ya ce ya tabbata a kan gwamnonin mu: ‘ya’yan talakawa da gwamnonin mu suka hana su karatu da sana’o’i, watarana za su zamo bala’i ga shugabanni da iyalansu. Allāh SWT ya kiyaye mu.
*Dabara ta rage ga mai shiga rijiya.*
Prof. Sulaiman Abdullahi Karwai
Department of Business Administration
Faculty of Management Sciences
Ahmadu Bello University,Zaria
Juma’a 7/11/1447 (24/4/2026)

